“Idan Mukaci Zabe zamu samar da Kamfani ko na Gwamnati ko na ‘Yan Kasuwa da zasu Dunga Sarrafa kayan Noma a Karamar Hukumar Bakori.”
Inji Sanata Yakubu Lado
Dantakarar Gwamnan jihar Katsina na jam’iyyar PDP Sanata Yakubu Lado ne ya bayyana haka ga magoya bayansa a Karamar Hukumar Bakori ranar Lahadi a lokacin da yake gangamin yakin Neman zabensa nan da Mako biyu masu zuwa.
Dantakarar ya yaba kwarai Dimbin Al’umma magoya bayan PDP da suka tarbeshi da nuna goyon bayansu gareshi tun a busa hanya kafin shiga garin na Bakori.
Sanatan ya jajanta da Addu’a ga mutanen da ‘Yan Bindiga suka kashe a Karamar Hukumar makon da ya wuce har mutum kusan dari, inda ya tabbatar da cewa zai bawa tsaro matukar muhimmanci da raimakon Gwamnatin Tarayya. A karshe yayi kira da zabar jam’iyyar PDP daga sama har kasa.
Daga cikin tawagar da suka dafa masa a wajen taron akwai Sanata Tsauri, shugaban yakin Neman zaben, da Dakta Mustafa Inuwa, Birgediya Maharazu tsiga, Dakta Musa Gafai (Ladon Alkhairi) da sauransu.