
Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News, 28/02/2023
A ranar Litinin kwanaki biyu bayan Kammala Babban Zaɓe a Najeriya, Jam’iyyar PDP a jihar Katsina da ‘Yantakararta, sun kira Taron Manema Labarai, don gidiya da bayyanama Al’umma daga ina aka fito ina kuma ake so a tafi a Zaɓukan da suka gabata da waɗanda zasuzo na Gwamnoni a watan Maris 11 gareshi.
Bayan bangajiya da godiya daga Shugaban yaƙin neman zaben Atiku/Lado, tsohon Sakataren Jam’iyyar PDP na ƙasa, Sanata Umar Ibrahim Tsauri, Babban Darakta na Yaƙin Neman Zaɓen kuma tsohon Ɗan takarar Gwamnan jihar Katsina, Dakta Mustafa Mohammed Inuwa, yayi magana a madadin Jam’iyyar PDP ta jihar Katsina.
Dakta Inuwa ya bayyana godiya da Jin dadi na yanda aka gudanar da zaben Lami lafiya. Sana ya bayyana rashin jin dadi da fargabarsa ganin irin yanda aka tafka son zuciya da rashin Adalci a zaɓen. Yace “A baya ganin irin yanda Shugaban ƙasa yace yanaso ayi Sahihin Zaɓe mai inganci, kuma ganinsa a matsayin Dattijo yasa muka yadda muka bada Amana don hakama yasa wasu Rumfunan ko wakili bamu tura ba, Amma sai mukaga sabanin abinda muka zata, ana saura kwana biyu zabe, aka je aka kama yarammu su goma sha hudu, aka aka watsamana Ɗakin Kwamfuta da na’urorin zamani da zamu dunga amsar sakamakon zaɓe kamar yanda Doka ta bamu dama. Sana kuma anga irin yanda ake murɗe sakamakon Zaɓe ƙarara, a ɗauki sakamakon PDP abawa APC a ɗauki na APC a bawa PDP, wannan Zalumci ne.” Inji Dakta Inuwa
Ya ƙara da cewa a wasu Rumfunan ma Ɓarayi Bandit ake turowa su kwashe sakamakon zaɓen, inda ya bada misali da ƙaramar hukumarsa ta Ɗanmusa.
Mustapha Inuwa yace, sun samu karfin gwiwa na fitowa su Kare ƙuru’unsu, a zaɓuka masu zuwa na Gwamna da ‘Yan majalisu, sana kuma a iya abinda akayimasu na maguɗi da ƙarfa-ƙarfa zasu zauna a matakin Jam’iyya suga hanyar da ta dace da Shari’a zuwa Kotu.
Dantakarar Gwamnan jihar Katsina Sanata Garba Yakubu Lado ya bayyana cewa an kwashe masa duka jami’an tsaro dake kula dashi, saboda wata manufa da ake son cimmawa don haka yanaso ya shedawa al’umma cewa duk abinda ya sameshi Gwamnati ce.
Alhaji Surajo Aminu Maƙera Ɗan takarar Sanata daga Mazaɓar Katsina ta Tsakiya ya bayyana irin Jindadinsa ganin yanda Al’umma suka fito suka zaɓeshi, amma aka kwace, yace yana godiya sana kuma zasu dauki matakin Shari’a a jam’iyyance.