A ranar Alhamis 25 ga watan Agusta masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a mazabar Jibiya Ward A mazaɓar mataimaki na musamman ga Gwamnan Katsina Aminu Masari a kan Kwadago, Alhaji Aminu Danmalikin Jibiya, sukayi zama na musamman domin tattauna abinda suka kira Zagon kasa wa jam’iyyar APC da suka ce Aminu Danmaliki yanawa jam’iyyar.
Kamar yanda Sakataren jam’iyyar a mazaɓar Jibiya Ward (A) Mazaɓar S.A na Gwamna Masari ya yace: “Sun gano Alh. Aminu Danmaliki yana so yayi Anti Party wa jam’iyyar APC don haka suka yanke shawarar Korar sa daga jam’iyyar a mataki na Ward. Babangida S. Abdullahi shine Sakataren jam’iyyar na Ward (A) Jibiya Local Government, yace dukkanin su sun sanya hannu sun samu matsaya su Ashirin da takwas inbanda mutum biyu, don haka daga ranara Alhaji Aminu Lawal Danmaliki Jibiya ba Dan jam’iyyar APC bane. Ya zuwa yanzu bamuji ta bakin Alh. Aminu Lawal ba akan wannan mataki da jam’iyyar a mazaɓar sa ya bayyana ba.