Gwamnonin PDP Guda biyar masu biyayya ga Wike sun bayyana ficewa cikin tawagar yakin zaben shugaban kasa Atiku na jam”iyar su ta PDP har sai an cika musu sharadin su.
Gwamnonin sun yi wani taro a jihar Benue Yanda Gwamna Samuel Ortom ya karbe su.
Gwamnonin sun hada da Gwamna Wike na jihar Ribas da kuma gwamna da Ortom, na jihar Benue gwamnonin da ake kira G-5 sun haÉ—a da, Seyi Makinde na jihar Oyo, Okezie Ikpeazu na jihar Abiya da Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa gwamnonin da dukkanin masu goya musu baya sun tsame hannu daga kwamitin yakin neman zaÉ“en shugaban Æ™asa na jam’iyyar PDP.
Sai dai sun kafa sharadin su kan cewa dole ne shugaban jam’iyya PDP na Æ™asa, Dakta Iyorchia Ayu, a cire shi a matsayin shuga hakan shine hanya É—aya tilo ta samun zaman lafiya a jami’iyar PDP in jisu.
Sai dai É—an takarar shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, a wata hira da kafar VOA Hausa tayi dashi yace sauya shugabancin PDP a halin yanzu ba abu ne mai yuwuwa ba.
Tsohon mataimakin shugaban kasan yace tuni ya tsallake daga matakin rikicin ciki gida ya ci gaba da harkokin tunkarar babban zaɓe mai zuwa.
Ko yaya kuke kwallon rikicin na PDP?