Farfesa Jega yaja hankalin Hukumar INEC da ta kauda kai da duk wasu ‘Yansiyasa dake hura wutar kadda ayi Amfani da Na’urar nan ta kada kuri’a ta zamani da za a gudanar da zabe da a ita a 2023. A zantawar da tsohon shugaban INEC yace: ganin yanda zaben ya kasance ‘Yan Watanni kadan ne suka rage a gudanar da shin, ‘Yan Siyasa zasuci gaba da nuna Bukatunsu na sonkai, don haka akwai bukatar Hukumar tayi taka tsantsan tare da kawar da kai ga duk wata Barazana da ka iya tasowa daga É“angaren ‘Yan Siyasa, kamar yanda Farfesa Jega ya bayyana a halin yanzu hukumar ta INEC nada hurumin yin amfani da Na’urar kamar yanda ta samu amincewa a doka da kuma tabbatar da cewa babu wata barazana da zata sanya taki aiwatar da abinda doka ta amince da shi, ya kuma bukaci Majalisar Dokoki ta kasa da ta tabbatar da sunayen mutanen kirki da zasu zama Kwamishinoni na hukumar zabe a jihohi.