Wasu Matasa masu fafutukar ganin Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu ya bar kujerarsa ta shugabancin jam’iyyar PDP, karkashin jagorancin Comrade Shehu Isah Dan’inna, sun gudanar da zanga-zangar lumana a garin Katsina, domin nuna kin amincewarsu da jagorancin Ayu.
Matasan da suka gudanar da zanga-zangar a jihohin Bauchi, Kano, Jigawa da Katsina sun yarda zasu zagaye Arewacin Najeriya domin nunawa Duniya cewa, Ayu bai dace ya zama shugaban PDP ba.
Shehu Isa Shine yake jagorantar Zanga-zangar yace; “Dattako ne ga shi shugaban jam’iyyar PDP Mista Iyorchia Ayu, a matsayin sa na Dattijo ya cika alƙawarin da ya dauka na cewa, idan har aka fidda Ɗantakarar Shugabancin ƙasa daga Arewa zai sauka daga mukaminsa.” Yace kin sauka daga shugabancin kamar rashin mutumtaka ne da girmama shekarunsa.
Matasan da suka shigo garin Katsina daga jihar Kaduna, sun bayyana cewa su ‘Yan PDP ne na hakika da suke son gyara domin kaucewa Faduwa Zabe, sunce duk wanda yaga yanda Obi na LP ya gudanar da Zanga-zangar sa ta Lumana a Abuja da irin yanda ya tara jama’a Magoya baya, yasan cewa akwai Babbar barazana a zaben 2023. A ƙarshe sunyi kira da dukkanin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP da su shigo su sanya baki a cikin sha’anin domin cimma Nasara

