Daga Mohammad A. Isa, Katsina.
Wasu manyan kungiyoyin Jam’iyyar PDP a jihar Katsina, sun doki kirji tare da shan alwashin kawo rumfunan zabuka tare da samun nasararorin jam’iyyar adawa ta PDP a jiha da ma kasa baki daya.
Gamayyar kungiyoyin Ladon Alkhairi da kungiyar nan mai rajin tallata dan takarar jam’iyyar PDP a Kasa ‘PDP National Youth Vanguard Katsina State Chapter’ a turance ne suka bayyana haka a yayin wani taron sada zumunci da hadin gwiwa a ranar Lahadi.
A yayin da yake jawabi a taron, shugaban kungiyar ta ‘PDP National Youth Vanguard’ na jihar Katsina, Alhaji Umar Misbahu Mai Zare, ya ce sun yi wannan hada-ka ne na hada hannu da karfe domin cin nasarar zabukan 2023 da ake fuskanta, inda a cewarsa za su kawo wa jam’iyyarsu ta PDP rumfuna a kowane mataki a jiha da kasa baki daya.
“Muna da Capacity da za mu hada hannu da karfe domin kawo nasarar jam’iyyar PDP a kowane mataki a Nijeriya.” Ya doki kurji.
Ya ci gaba da cewa, “Babu wanda zai kalli mulkin da PDP ta yi wanda Matawallen Katsina Alhaji Umaru Musa ‘Yar’adua ya jagoranta shekara 8 ya ce akwai ragganci a cikinsa. Babu wanda zai kalli mulkin shekaru 8 da Barista Ibrahim Shehu Shema ya yi ya ce akwai raggwanci a cikinsa. Kuma kowa ya kallin wannan mulki da ake yi yanzu (na APC), ya san mulki ne wanda yake cike da raggwanci.” Ya gwalashe.
Shi ko a nasa jawabin, shugaban kungiyar Ladon Alkhairi, Honorabul Musa Yusuf Gafai ya bayyana jin dadinsa a kan yadda wannan kungiya wadda take uwa ga kaf din kungiyoyin jam’iyyar PDP, amma ta karbi kungiyarsa ta kuma ba ta muhimmancin gaske har suka dauke ta a matsayin lamba daya a wajensu, inda ya bayyana hakan a matsayin jam’iyyar PDP ce mai nasara a zabukan 2023.
Musa Gafai, ya kuma karfafa ‘ya’yan kungiyoyin biyu da duk wani dan jam’iyyar PDP da cewa; “kar mu bari abin nan (mulkin APC) ya zarce!”
A yayin taron hadin gwiwar kungiyoyin biyu, kungiyar Ladon Alkhairi, ta bada takardar ‘appointment’ na wasu mukamai, muhimman takardu da ‘Tags’ na girmamawa ga wasu ‘ya’yan kungiyar ta National Youth Vanguard.