
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta a Najeriya ta ƙaryata wasu labarai da ke yawo a wasu shafukan sada zumunta da cewa hukumar ta saki sabbin sunayen ƙarshe na ‘yan takara gabanin babban zaɓen ƙasar da ke tafe.
A wani sako da hukumar ta fitar mai ɗauke da sa-hannun shugaban kwamitin yaɗa labarai da ilimantar da masu jefa ƙuri’a Festu Okoye, aka kuma wallafa a shafin hukumar na Tuwita, hukumar ta ce tana so ta bayyana wa al’umma ƙarara cewa babu wasu sabbin sunayen ‘yan takara da ta fitar kamar yadda rahotonnin ke bayyanawa.
Saboda haka hukumar ke kira ga jama’a da su yi watsi da labarin. Domin kuwa a cewar sanarwar hukumar zaɓen kan fitar da sunayen ƙarshe na ‘yan takara kwanaki 150 kafin ranar zaɓen kamar yadda sashe na 32(1) na dokar zaɓe ta 2022 ta tanadar.
Sanarwar ta kuma ce tuni hukumar ta fitar da sunayen ƙarshe na ‘yan takarar shugaban ƙasa tun ranar 20 ga watan Satumba, yayin da ta fitar da na ‘yan takarar gwamna ranar 4 ga watan Oktoba.
Dan haka ne hukumar ta ce babu wasu sunaye da za ta sake fitar wa a halin yanzu da ake saura kwana 46 a gudanar da babban zaɓen, sai dai sunayen ‘yan takarar da kotu ta bayar da umarnin maye gurbin sunayensu.