Daga Comr Nura Siniya
Ɗan takarar shugabancin Nijeriya na PDP Atiku Abubakar, ya kaddamar da ƙwamitin yaƙin neman zaɓen shi na 2023 mai ɗauke da mutane 545 yau Laraba a ɗakin taro na ƙasa da ƙasa ICC da ke birnin tarayya Abuja.

Haka zalika Atiku ya ƙaddamar da littattafan da ya rubuta guda 3 wanda suka ƙunshi bayanan hanyar da zai bi domin gina sabuwar Najeriya.
“A cikin Littattafan da Atiku ya rubuta, sun yi bayani akan tarihin rayuwarsa, tun daga malanta a makaranta, siyasa, zaman shi mataimakin shugaban ƙasa da manufofin sa da kuma kudurorin shi da suka ƙunshi tsaro, tattalin arziƙi, noma, haɗin kan ƴan Najeriya.
“A ƙarshe Atiku ya sha alwashin yaki da talauci da yunwa da suka jefa da yawan ƴan Najeriya cikin halin ƙuncin rayuwa.