Alh. Aminu Balele Kurfi (Ɗan’arewa) Ɗan takarar Kujerar Majalisar wakilai ta Tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Dutsin-ma da Kurfi, ya kaddamar da wani shiri na ɗaukar Mutane dubu 21 da zasu dafa masa a yaƙin neman zaɓen 2023 kuma zai dunga biyansu albashi a duk wata.
Dan Arewa ya fara bin Shiyyoyin mazaɓun domin ƙaddamar da mataimakan nasa, inda ya fara da Tsauri A, Birchi A, Rawayau A,da B, duk a cikin ƙaramar hukumar Kurfi.
Da yake jawabi a wajen taron, Alh. Aminu Balele Kurfi, ya bayyana jin dadinsa ganin irin goyon bayan da yake samu ga al’umma. Inda ya bayyana masu cewa “Dan Arewa ba raggo bane dan Arewa idan aka zaɓeshi za’asan Kurfi da Dutsin-ma sunyi Danmajalisa.”
Ya kara da cewa “Zamuje Majalisa zamu sanya ido dole sai anyiwa Jihar mu abinda muke buƙata, idan har ba’ayi mata ba to Ɗan’arewa ya iya Kife ya iya Birkice”
Yayi kira da a zaɓi APC daga sama har ƙasa, yace “Katsina Muna da Dattawa da ko basu Mulki sunfi ƙarfin suce ayi aƙi yi” yace akwai Aminu Bello Masari da Shugaba Muhammadu Buhari wadanda idan wani abu ya cakuɗewa Asiwaju dole ya dawo garesu su bashi shawara, idan suka bashi yaƙi ji, to zasu turamu muje muyi mashi da yaren da zai gane.” Inji Ɗan’arewa. Yace a Tambayi Mantu da Obasanjo aji suwanene Aminu Masari, da Dan Arewa.
Bayan kaddamarwar amfara bawa ko wane Coodinator da aka zaba Alawus dinsa nan take, inda kuma Ɗan’arewa ya bayyana cewa shirin zai ci gaba. A wani Labarin kuma Alh. Aminu Balele Kurfi ya amshi fiye da Mutum hamsin daga cikinsu hadda Ciyamomin mazaɓu a Rawayau B. Da suka fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC Mai mulki duk a ranar Litinin inda Aminu Balele yayi alƙawarin tafiya dasu kafada da kafada da sanyasu tsarin mataimakansa a zaben 2023 da fara biyansu Albashi daga sati mai kamawa