Yarjejeniyar dakatar da ɓude wuta ta kwanaki uku ta fara aiki a Sudan. Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ne ya sanar da hakan, inda ya ce dakarun RSF sun amince da tsagaita wuta daga tsakar daren jiya Litinin.
Ya ce an cimma nasarar ne bayan shafe kwanaki biyu ana abin da ya kira zazzafar tattaunawa, ciki har da wakilan ƙasashen Saudiyya da Amurka da kuma ɓangarorin sojin Sudan.
Sai dai babu tabbacin ko ɓangarorin biyu sun amince da hakan. Tun da fari duk kokarin da aka yi na dakatar da gwabzawa ya ci tura.
Kusan mutane 400 aka kashe a yakin da ya ɓarke kwanaki 11 da suka gabata, tsakanin dakarun sojin Muhammad Hamdan Dagalo da na Abdul Fatta Al-Burhan.