BBC Hausa
A ranar Juma’a ne Yarima Charles na Birtaniya zai je Rwanda domin radawa birrai suna a wani bikin dabbobin gandun daji da aka saba yi duk shekara mai suna Kwita Izina.
Wannan daya daga cikin bukukuwan yawon bude ido ne na Rwanda da take yi duk shekara wanda kuma ya samo asali daga al’adu da aka gada na radawa yara sabbin haihuwa suna.
Yariman zai kasance cikin manyan mutane masu fada aji a duniya guda 20 da za su halarci bikin. Amma zai halarci bikin ne ta hanyar intanet.
Zuwan karshe da Yarima Charles ya yi zuwa Rwanda shi ne a watan Yuni lokacin da ya halarci zaman tattaunawa na shugabannin gwamnati na kasashen renon ingila Commonwealth.
Yariman dai yana da sha’awar dabbobin da ke zama a gandun daji.
Wannan ne karon farko da za a gudanar da bikin cikin taron jama’a tun 2019 bayan barkewar annobar corona.