Majalisar wakilai ta bukaci Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya dakatar da aiwatar da sabuwar dokar ƙaiyade cire kudaden, wacce aka shirya gudanarwa a ranar 9 ga watan Janairun 2023 har sai an cika sharuddan dokar da ta kafa bankin.
Hakazalika, majalisar ta kuma gayyaci gwamnan babban bankin na CBN, Godwin Emefiele kamar yadda dokar babban bankin kasar ta tanada domin ya yi wa majalisar bayani kan manufofin bankin da dama a kwanakin baya.
An dai fusata ne a zauren majalisar a yau Alhamis, yayin da ƴan majalisar ke bi da bi suna yin Allah -wadai da sabuwar manufar cire kudaden, suna masu cewa hakan zai yi matukar shafar kananan masana’antu da tattalin arziki ‘, tunda akasarin al’ummomin karkara ba su da damar yin harkar banki.
Sai dai kuma bayan wani batu da Mark Gbillah ya gabatar kan tanade-tanaden dokar babban bankin kasar, majalisar ta umurci Gwamnan CBN da ya gurfana gabanta a ranar Alhamis, 15 ga watan Disamba, 2022 domin yi wa majalisar bayani kan dalilin da ya sa dokar za a bar ta ko akasin haka.