Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Baba, ya bayar da umarnin tsare mawakan Afrobeat, Seun Kuti, bisa zargin cin zarafin wani dan sanda a Legas,kamar yadda Punch ta rahoto.
IG din ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike cikin sauri kan musabbabin kai harin da kuma gurfanar da wanda ake tuhuma a kan haka.
Wannan dai na zuwa ne kamar yadda mawakin ya yi zargin yunkurin kashe shi da iyalansa da dan sandan da ake magana a kansa inda ya wallafa a shafin sada zumunta da wakilinmu ya samu a daren ranar Asabar.
Da yake magana kan lamarin a cikin wata sanarwa da wakilinmu ya samu a daren ranar Asabar da ta gabata, jami’in hulda da jama’a na rundunar, Olumuyiwa Adéjọbí ya ce,
“Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Baba, ya umarci kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas da ya kama mawakin Afrobeat. Seun Kuti, wanda aka dauka a faifan bidiyo yana cin zarafin wani jami’in dan sanda sanye da kaki.
“IG din ya kuma ba da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa kan musabbabin harin da kuma gurfanar da wanda ake tuhuma a kan haka.
“Baba ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa ba za a amince da ayyukan raini ko kyama ga alamomin hukuma ba, yayin da za a gurfanar da masu aikata irin wadannan manyan laifuka.”
A halin da ake ciki, a wani sako da ya wallafa a daren ranar Asabar a Instagram wanda wakilinmu ya samu, Ṣeun Kuti ya lura cewa dan sandan da ake magana a kai ya nemi afuwa kan zargin yunkurin kashe shi da iyalansa.
Kuti ya ce, “Ya yi kokarin kashe ni da iyalina. Ina da hujja amma ba ni da fata.
“Ya ba da hakuri kuma na amince ba zan tuhume shi ba. Kada ku manta da kasuwanci kada talaka ya rasa aikinsa.”