DA DUMI-DUMINSA| Hukumar Zabe Ta Kasa Ta Fitar Da Sunan Shekarau A Matsayin Dan Takarar Kujerar Kano Ta Tsakiya A Jamiyyar NNPP
A Yau ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta Fitar da Sunaye na Karshe na Yan Takarar karun Majalisar Tarayya, Sai dai Abun Mamaki Yadda Aka Fitar da Sunan Mal. Ibrahim Shekarau, a Matsayin Dan Takarar Jamiyyar NNPP, Duk da Shekarau, yafice Daga Jamiyyar, Kuma sun sake Zaben Cikin Gida Wanda suka Ayyana Rufa’i sani Hanga, A Matsayin Wanda zaiyi Takarar.
Wasu rahotanni na bayyanar cewa Hukumar Zabe ta Kasa Bata Karbi Sunan Dan Takarar Jamiyyar NNPP, da Aka tura mata ba Bayan Fitar Shekarau, Daga Jamiyyar.
Vanguard Hausa
