Gwamnatin Jihar Katsina tayi sauyin wurin aiki ga wasu ƙwamishinoni tare da sallamar wani Babban Darakta, a takardar da Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina Alh. Muntari Lawal ya sanyawa hannu ta bayyana cewa an sauya ma ƙwamishinan Matasa da Wasanni Hon. Gambo Saulawa wurin aiki daga Ma’aikatar zuwa Ma’aikatar Land and Survey.
Yayinda Ƙwamishinan na Land and Survey kuma aka maida shi zuwa Ma’aikatar Special Duty.
Haka nan kuma Gwamnatin ta miƙa sunan Hon. Sani Danlami zuwa Majalisar jihar domin tantance shi a matsayin ƙwamishina.
Kazalika Gwamnatin ta bayyana cewa ta gimtse aikin Alh. Babangida Nasamu tare da Maye gurbin shi da Hon. Haruna Musa a matsayin Shugaban Hukumar SEMA
