Magoya bayan jam’iyyar adawa ta NNPP a jihar Kano sun fara zanga-zanga kan shirin kawo Balarabe Sule, tsohon babban jami’in tsaro na gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, zuwa Jihar Kano a matsayin kwamishinan ‘yan sanda.
Tsohon shugaban hukumar TETFUND, kuma tsohon ɗan takarar Sanata na Kano-ta-Arewa, Baffa Bichi ne ke jagorantar zanga-zangar.
DAILY NIGERIAN ta samu rahoton cewa masu zanga-zangar sun yi tsinke a shelkwatar ƴansanda ta shiyya da ke kan titin BUK a kwaryar birnin Kano.
Tun a jiya Litinin ne wasu sahihan majiyoyi su ka shaida wa DAILY NIGERIAN cewa in dai ba wani canji aka samu ba, Sufeto-Janar na ƴansanda zai kawo Balarabe Sule ya maye gurbin Mohammed Yakubu, wanda aka tura jihar makonni biyu kacal da suka wuce.
Wasu daga cikin ‘yan sanda sun tabbatar wa DAILY NIGERIAN cewa, Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali, ya bayar da umarnin tura jami’in ‘yan sandan jihar, biyo bayan matsin lamba da jam’iyya mai mulki ta ke yi masa.
Majiyar mai tushe ta shaida wa wannan jarida cewa za a tura MSule zuwa jihar Kano tare da ACP Abubakar Shika da ACP Adamu Babayo.
Sule, wanda a kwanan nan aka kara masa mukami zuwa na kwamishinan ƴansanda, aka kuma kai shi jihar Cross River, ya kasance mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da ayyuka a Kano tsawon shekaru da dama.
A cewar masu lura da al’amuran cikin gida, jami’an ukun, wadanda dukkansu suka yi aiki tare, an yi musu tambarin da cewa su na da bamgaranci na siyasa, inda da ake amfani da su wajen murkushe ‘yan adawa.
Majiyoyin sun shaidawa DAILY NIGERIAN cewa wannan wani shiri ne ke yi wajen sarautar da martabar aikin su domin hada kai da ƴan siyasa wajen murkushw jam’iyyun adawa.
A tuna cewa a sake zaben gwamna na 2019, an hada kai da ƴansanda wajen bai wa ‘yan baranda masu biyayya ga jam’iyya mai mulki damar hargitsa zaben, tare da kai wa masu kada kuri’a, masu sa ido kan zabe da ‘yan jarida hari.