Muhammad A. Aliyu @ Katsina City News
A wani Faifen Bidiyo da yake yawo a kafafen sada zumunta na zamani anjiyo Mawakin Siyasa Dauda Rarara yana bayyana shaguɓensa ga Hukumar ‘Yansanda akan wani Faifen Bidiyo da ya nuna wanda ke gwada wasu jami’an ‘Yansanda a farfajiya wani gida ko ma’aikata suna harba harsashi mai rai a sama ba tare da wani dalili ba, kwatankwacin irin yanda wasu ‘Yansanda da Rarara ya kira yaransa suka Aikata a garin Kahutu a lokacin da suke rakiyar Mawakin zuwa wajen rabon tallafin Azumi, aka koresu.
…duk inda zankai kuka na don kada a koresu naje abin ya gagara”
Dauda ya bayyana a cikin bidiyon cewa “Ina rokon hukumar ‘yansanda da kada ta kori wadannan bayin Allah, saboda basu da kowa, idan aka koresu ina zasu sanya kansu?” Yace “Nidai yarana sunada ni, kuma nayi Alkawarin zan dunga biyansu abinda ake basu na Albashi daga yanzu har inmutu, saboda naje duk inda zanje nemar masu Alfarma don abarsu da aikinsu amma abin yafi karfina.” Injishi.
An tambayi Rarara cewa “bidiyon da ya nuna a akwatin Talabijin baya nufin shagube ne ga Hukumar? Sai yace shi ba shagube bane, amma idan har za a kori yaransa (Yansanda) daga Aiki don sun harba bindiga sama, to ga wasu suma sunyi irin lafinda da yaransa (‘Yansanda) sukayi idan har ba’a koresu ba to kenan da wata manufa akayi.
Yace babban Albishir da zaiyi akan masu wannan Kore-koren Baba na zuwa.
Abinda wasu ke tambaya anan shine, shin su wadannan jami’an tsaro dama yaran Mawakin Siyasa Daura Rarara ne, kamar yanda ya bayyana da bakinsa ko kuwa jami’an tsaron ƙasa ne suna kare rayukan ‘yan ƙasa? Sana kuma idan har yaranshi ne kamar yanda ya bayyana to umarninsa suke bi ba na hukumar da sukewa aiki na tsaro ba, don haka sun cancanci kora, saboda sun koma karkashin wani wanda ba Dansanda ba, kuma suna ɗauke da makami, wanda hakan saba ƙa’ida ne.
“Ta tabbata Yaransa ne, tunda gashi har ya dauke masu Albashi wanda suke amsa ga Hukumar ‘Yansanda, don gadara haka kuma laifi ne, shi kansa ya aikata ga Hukumar da kuma raina hukumar” inji wani da ya nemi mu sakaya sunansa da muke jin ra’ayin jama’a game da batun.