Kamar yadda ake yakin neman zabe muma haka zamu tashi yakin nemama addini mafita a cikin wadanda zamu zaba. ‘Inji” Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina.
Ibrahim Nasir Faskari
Sheikh Yakubu Musa ya fadi haka ne ranar Asabar 26-11-2022, yayin kaddamar da kwamatin da kungiyar izala ta kafa domin tunkarar zaben shekara 2023, a dakin taro na “Service to humanity”, dake Katsina.
Ya cigaba da cewa” mun taru ne nan domin tattauna wasu muhimman abubuwa dan gane da zaben da muke tunkara. Domin duk al’amur ran rayuwa babu inda addinin musulunci bai tabo ba.
Kuma ita wannan kungiya ta izala Allah ta’ala yayi mata baiwa, domin bayan da’awa da takeyi tana tabo abubuwa da su ka shafi rayuwar alumma kamar siyasa, kiwon lafiya. Da dai sauransu.
Wannan yasa matsayinmu na musulmi ya kamata mu tsaya muyi duba da irin shugaban nin da yakamata mu zaba domin kare martaba da kimar addinmu.
Amma mu sani kungiya na nan na jiran umarni daga sama akan wanda za’a goya ma baya. Haka zalika matsayin mu na musulmi kamar yadda ake yakin neman zabe muma haka zamu tashi yakin nemama addini musulunci mafita.
Shima da yake gabatar da jawabinsa, Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari wanda yasamu wakilcin mai taimaka masa akan harkokin tsaro Mal.Ibrahim Katsina.
Ya bayyana cewa” wannan yunkuri da kungiyar izala tayi yunkuri ne, mai kyau domin ko babu komi hanya ce da musulmi zasu nemama kansu mafita.
Kuma Insha Allah zasu shiga cikin tsari suma a tafi dasu domin ganin an kai inda akeson akai da izinin Allah. Fatan Allah ya maida kowa gidanshi lafiya.
Malamai da dama ne, su ka gabatar da nasihohi a wurin taron daga cikinsu akwai Mal. Shafi’u Alkasim, Malam Abdulrahim Sabi’u, Saifuddin Yakubu Musa.
Abubakar Yusuf Saulawa Mai baiwa Gwamnan Jihar Katsina shawara akan bunkasa kasuwan ni. Da dai sauransu.Taron yasamu halartar shuwagabannin kungiyar na jiha da na kananan hukumomi shuwagabannin malamai da dai sauransu.