A ranar Lahadi 28 ga watan Disamba ne Jam’iyyar APC ta kawo karshen zagayen yakin neman Zaɓen ta ba Shiyyar Daura wato (Daura Zone) wanda aka karkare a garin Kankia.
Gwamnan Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari na daga cikin wadanda suka halarci taron rufe yakin neman Zaɓen na garin Kankia kuma ya bayyana jin dadin sa ganin irin yanda al’umma kwai da Kwarkwata suke cincirindo don tarbar Dantakarar Gwamnan na Katsina Dakta Dikko Umar Raɗɗa, Gwamnan yace “na tabbatar da cewa Al’umma suna tare da mu, suna tare da APC don haka muna godiya.” Injishi Gwamna Masari ya bayyana cewa akwai maganganu amma sai idan Allah ya kaimu ranar rufe taron gangamin a Katsina.
Zagayen yakin Neman zaben na Dantakara Gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar APC Dakta Dikko Umar Raɗɗa da aka fara da ƙaramar hukumar Baure bayan taron kaddamarwa a karamar hukumar Faskari, inda aka karkare a karamar hukumar Kankia tare da rakiyar Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar daga fadin jihar Katsina kungiyoyi ‘Yan jaridu da sauran Al’umma, an zagaye mazabu fiye da dari kuku na ƙananan hukumomn 11 gami da alkawurra da gabatar da kudirirrika na cigaba idan Allah ya bawa Dantakarar dama na zama Gwamnan jihar Katsina a 2023.