Asirin wani tsohon Soja ya toni Inda Jami’an tsaron Ƴansanda sukayi nasarar chafke shi yayinda yake kan hanyar shi ta safarar Makamai zuwa jihar Zamfara daga jihar Nasarawa.
Wanda Jami’an tsaron suka kama tsohon Soja Cpl Sa’idu Lawal Ɗan kimanin Shekaru 41 a Duniya an kamashi da abubuwa kamar haka;
1 AK-47 Rifle Breech No. Q971987
1 AK-49 Rifle Breech No. 34-7094
200 7.6mm Rounds of Live Ammunition
501 7.62X51mm Rounds of GPMG Live Ammunition
8 Empty Magazines

Lamarin rashin tsaro dai yana Ci gaba da addabar Jihohin Zamfara, Katsina, Kaduna, Niger, Kebbi da jihar Sokoto, a ranar 27th August, 2022 da misalin ƙarfe Biyar da Rabi na Yammaci Jami’an Ƴansanda da suke aiki tare da ƙwamishinan ƴansandan jihar Zamfara, CP Kolo Yusuf psc suka samu bayanan sirri da sukayi sanadiyyar kamun tsohon Sojan Wanda yayi aiki ƙarƙashin Bataliya ta Saba’in da Ukku 73 dake Barikin Sojoji ta Janguza jihar Kano.
An dai kama Wanda ake zargin ne da Mota ƙirar Pontiac Vibe Mai ɗauke da lamba KRD 686 CY Lagos, akan hanyar Abuja – Kaduna bisa hanyar shi ta zuwa jihar Zamfara, yayinda aka bincike shi shine aka samu waɗannan Miyagun Makamai a tare dashi.
Yayin da yake amsa tambayoyin Jami’an tsaron ya tabbar da cewa ya ɗakko waɗannan Makamai ne daga ƙaramar hukumar Loko ta jihar Nasarawa zai kuma kaisu ga wani Dogo Hamza dake ƙauyen Bacha cikin ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
Wanda ake zargin ya tabbar da cewa a baya ya zamo mai Safarar Makamai a Jihohin Kaduna, Katsina, Niger dama jihar Kebbi Jami’an tsaro sun tabbar da cewa suna bincike domin samun sauran Abokan ta’adancin nashi.