Yan takarar gwamnan jihar Katsina kalkashin jam’iyyu daban daban sun rattaba hannu akan wata takardar yarjejeniyar zaman lafiya gabanin da kuma bayan zaben dake tafe wanda za’a gudanar a fadin kasar
Taron kulla yarjejeniyar ya gudana ne a birnin Katsina karkashin jagorancin rundunar yan sandan jihar
Da yake jawabi jim kadan kafin yan takarar su rattaba hannu akan takardar yarjejeniyar, kwamishinan yansandan jihar Katsina C.P. Shehu Umar Nadada ya bayyana cewa an tara yan takarar ne domin su kara amincewa da juna tare da tabbatar ma junansu amincewa a gudanar da zaben cikin zaman lafiya da lumana, tare da kauracema duk wani abu na zai gurgunta sahihancin zaben kafin da kuma bayan zaben
Kwamishinan wanda ya samu wakilcin mukaddashin kwamishin yansanda DCP Shattima Muhammad Durtu ya bayyana yarjejeniyar a matsayin wani aminci tsakanin yan takarar domin tabbatar an gudanar da zabe cikin zaman lafiya da lumana, yana mai cewa
“Manufar taron nan shine domin karfafa zaman lafiya da mutunta juna a tsakanin yan takarar jam’iyyun siyasar da muke dasu, zai tabbatar da karin fahimtar juna duk da banbancin siyasa dake a tsakanin su.
Ya bada tabbacin rundunar wajen kasancewa mai adalci a tsakanin jam’iyyun daban daban ba tare da fifita daya daga cikinsu ba.
Kwamishinan yansandan yayi Kira ga yan takarar da su amince da sakamakon zaben na 2023 da za’a gudanar, yana mai fatan jam’iyyun da yan takarar zasu bi hanyoyin da doka ta amince wajen bin hakkin su ga wanda a bayan zaben zai ji cewa ba a yi mashi adalci ba domin tabbatar da zaman lafiyar al’umma
Shima a nasa jawabin shugaban hukumar zaben ta kasa a jihar Katsina Professor Yahayya Makarfi wanda ya samu wakilcin Isah Magaji Gumi ya bada tabbacin hukumar na gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaben da kowa zai amince dashi, yana mai Kira ga jam’iyyun da yan takarar su gudanar da harkokin siyassr su bisa tsarin tanadin doka domin cimma nasarar gudanar da zaben ba tare da fuskantar wata matsala ba.
A nasu jawabin a wajen taron, yan takarar, ta bakin dantakar gwamnan jihar Katsina kalkashin jam’iyyar SDP Alhaji Ibrahim Zakari sun bada tabbacin su na tabbatar da yin duk abinda ya dace wajen ganin magoya bayan su sun bi sharuddan yarjejeniyar da suka sanya ma hannu a wajen taron
Kazalika sun tabbatar da cewa zasu amince da sakamakon zaben ga duk wanda Allah ya baiwa nasara a tsakanin su tare da taya shi murna.
Wadanda suka sheda kulla yarjejeniyar a wajen taron sun hada da babban jojin jihar Katsina mai Shari’a Musa Danladi wanda ya samu wakilcin Magatakardan babbar kotun jihar Barrister Nura El ladan, da kungiyoyin fararen hula da hukumar zabe ta kasa INEC da kuma dukkanin hukumomin tsaron kasa da suka halarci taron
Sauran Abubuwan da suka gudana a wajen taron sun hada da rattaba hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya wadda yan takarar suka gudanar