
Daga Barrista Nuraddeen Isma’eel.
“Zanga-zangar adawa da EFCC ta koma zubar da jini, yayin da ‘yan sandan Najeriya suka bindige masu zanga-zangar 3 da kona motoci sama da 20 da masu zanga-zangar suka riƙayi.
“Zanga-zangar da matasa suka yi ranar Talata don nuna adawa da ayyukan hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC a jihar Delta ta rikiɗe zuwa tashin hankali”
“Masu zanga-zangar sun yi zargin cin zarafi, da kuma kame na al’umma da jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ke yi.”
“Sai dai ba’a jima ba zanga-zangar ta rikide zuwa tashin hankali inda aka kona motoci sama da 20 dauke da kayayyaki na miliyoyin naira.”
“Zanga-zangar wacce ta haifar da tashin hankali da firgici ta faru ne a mahadar Otovwodo da ke unguwar Ughelli a karamar hukumar Ughelli ta Arewa.
“An yi zargin cewa, akwai wasu da ake zargi da damfara ta yanar gizo wadanda aka fi sani da “Yahoo Boys” ne suka ƙaddamar da wannan zanga-zangar”
“ALFIJIR HAUSA ta tattaro cewa, sama da matasa uku ne ake zargin jami’an rundunar ‘yan sandan jihar ne suka harbe su”
“A halin yanzu dai wadanda abin ya shafa na cikin wani hali na barazana ga rayuwarsu a wani asibiti da ba a bayyana ba a yankin inda aka kai su asibiti.
“Matasan da suka gudanar da zanga-zangar sun kona wasu manyan motoci makare da granite da man fetur da dai sauran kayayyaki, inda suka kuma killace mahadar Otovwodo mai cike da cunkoson jama’a, Ughelli, a kan titin Gabas zuwa Yamma.”
“Masu zanga-zangar sun rera wakokin yaƙi yayin da suke kona tayoyi a hanyar da abin ya shafa.
“Gwanon zanga-zangar wacce aka yi wa laƙabi da ‘#EndEFCC’ ta fara ne da misalin karfe 11:00 na safe, wanda ya kawo cikas ga zirga-zirgar ababen hawa duk a jihar Deltan”
“Sun baje kwalaye masu rubuce-rubuce daban-daban kamar “#EndEFCC”, “EFCC, ku kyale mu, mu ba masu laifi ba ne”, da “A daina cin zarafi, cin zarafi, tsoratarwa da kamawa ba gaira ba dalili”