Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce jami’anta sun dakile wani harin da ‘yan ta’adda suka kai a ranar Juma’a a kauyen Dagwarwa da ke karamar hukumar Kurfi a jihar Katsina, inda suka kashe biyu tare da kwato shanun da aka sace da babur guda daya.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, CSP Gambo Isah ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, a yau Juma’a.
Ya ce, “A safiyar yau Juma’a 14 ga Afrilu, 2023, mun samu kiran waya cewa ‘yan bindiga da muggan makamai sun yi ta harbi da bindiga kirar AK 47, sun kai hari gidan wani Sarkin Fulani, a kauyen Danmarke, a gundumar DAGWARWA, karamar hukumar Kurfi. Jihar Katsina.”
Ya yi nuni da cewa, DPO na Kurfi shi ya jagoranci tawagar ‘yan sanda da ke sintiri zuwa yankin, inda suka yi artabu da ‘yan ta’addan tare da samun nasarar fatattakar su.
Ya ci gaba da cewa, anyi Nasara, an kashe ‘yan ta’adda biyu tare da kwato duk shanun da aka sace.
“Da yawa daga cikin ‘yan ta’addan ana kyautata zaton, an kashe su, ko kuma sun tsere da Muggan raunika na harbin bindiga.
Ya kuma yi kira ga al’ummar yankin da su kai rahoto ofishin ‘yan sanda mafi kusa da duk wanda aka samu ko aka gani da wani abin da ake zargin ya samu rauni.