Muhammad Ahamad Ali
Allah mai yanda yaso a lokacin da yaso mai bada mulki ga wanda yaso ya amsa ga wanda yaga dama, ko ya amsa kana raye ko ya amsa ya kiraka zuwa matabbata (Mutuwa) A farkon Shekarar nan ta 2022 Allah ya nuna Kudirar sa ta hanyoyi da dama daga ciki Akwai Annobar Amai da gudawa da akayi fama da ita a wasu jihohin Najeriya, Ammabaliyar ruwa kuwa ko a lokacin hada wannan rubutu wasu jihohin suna cen suna tattara kayansu, Ansamu rashe-rashe na Mutane daban-daban ta hanyoyi daban-daban kama daga hanyar masu garkuwa da mutane, zuwa Hatsarin Mota, Mutuwar Fuj’a da doguwar Jinya. A cikin wannan Shekarar ne, aka rasa Manyan Malamai Sarakuna da Attajirai. Kamar Shekarun baya wato a Shekarar dubu biyu da Ashirin daidai a cikin watan Mayu Allah ya karbi rayuwar Danmajalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Bakori, a majalisar jihar Katsina, Marigayi Alhaji Abdulrazaq Tsiga. Bayan rasuwar sa, kamar yanda dokar kasa ta tanada aka bawa masu sha’awa damar neman Kujerar sa ta Majalisar Jiha, inda Hon. Alhaji Dakta Ibrahim Aminu Kurami ya samu Nasarar lashe Zaben Danmajalisar. Dakta Kurami an shede shi da hakuri Mutumtaka, da kuma jajircewa wajen kwatowa Al’umar yankinsa Hakkokin su da ya rataya a kansa a matsayin sa na Danmajalisar karamar hukumar Bakori. Anjiyo wani bidiyo da Kafar yada labarai ta Katsina City News ta saki inda Dakta Kurami yake magana a gaban Zauren majalisar dokokin jihar Katsina, bisa ga sakacin jami’an tsaro na kare rayukan Al’umma. Dakta Kurami a cikin Bidiyo yayi Kausasan Kalamai ga jami’an tsaro musamman ga Sojoji da zarge-zarge yayi yawa akansu na sakaci da Amanar da aka damƙa ta rayukan Al’uma garesu. Da wannan kalaman ne ake ganin Dakta kurami baije majalisa domin Dumama kujera ba, yana iya kokarinsa na ganin Al’umar yankinsa sun samu Kwanciyar hankali da Aminci.
A ranar Lahadi 9 ga watan Oktoba Allah yayiwa Danmajalisar Dakta Ibrahim Aminu Kurami rasuwa a kasara Saudi’arebiya bayan zuwansa Aikin Ibadar Umra. Muna fata Allah ya karbeshi a matsayin Shahidi, Allah ya bawa iyalansa da Al’ummar Jihar Katsina Hakurin jure rashin. A yau Talata 11 ga watan Oktoba muna saura Kwana. 136 a yi Babban Zaben ƙasa na Shugabanni, Gwamnoni, da ‘Yan Majalisar su. Shin ko cike gurbin Dakta Kurami zai iya yiyuwa kafin wannan ‘Yan kwanaki da suka rage? Idan har aka gaza haka mi Dokar kasa ta tanada a akan wannan wawakeken gibi da zai iya kawoma karamar hukumar Bakori gagarimin ci-gaba, idan an samu irin Kurami, idan kuma akasin haka koma aka gaza yin zaben cike gurbin mi zai haifar?