‘Yan bindiga sun sace Tsohon Daraktan Kula da Ma’aikata na Jihar Neja, Alhaji Usman Abdullahi Malami da Likitan dabbobi, Musa Mohammed, da ke Ma’aikatar kula da dabbobi, tare da wasu mutane 50 da’ yan bindiga suka sace a jihar Neja.
Rahotanni sun tabbatar da cewa, ‘yan bindigar sun sace mutanen ne a yankunan Kananan Hukumomin Kontagora da Munya.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa masu garkuwa da mutanen sun sace Malami ne ranar Juma’a a lokacin da yake dawowa gida a hanyar Kontagora-Mariga, tare da wasu ma’aikatan da suke aiki tare da shi.
Shi ma Dakta Muhammad an sace shi ne a kan hanyar dawowa Kontagora daga kauyukan yankin inda ya je don yi wa dabbobi allura.
Daga bisani ‘yan bindigar da suka sace mutanen sun kira iyalansu, inda suka nemi a biya su Naira miliyan 15 a matsayin kudin fansa.
A ‘yan kwanakin nan dai ‘yan bindiga sun matsa kaimi wajen kai hare-hare kan jama’a a kan hanyoyin Kontagora-Mariga da Kontagora-Rijau, inda suke kashewa da sace jama’a.
A wani labarin kuma, ‘yan bindigar sun sace mutane 50 a garuruwan Kuchi a Karamar Hukumar Muna a Jihar Neja.
A wata sanarwa da jami’in gudanarwa na kungiyar matasan Shiroro
(Concerned Shiroro Youths), Sani Kokki, ya raba wa manema labarai, ya ce an sace mutanen ne da karfe 2 na daren Juma’a.
“Mun samu rahotannin da ke tabbatar da cewa ‘yan ta’adda masu yawan gaske sun kai hari wasu kauyuka a yankin Kunchi a Karamar Hukumar Munya a tsakar dare, inda suka sace mutane masu yawan gaske”, in ji shi.
Kokki ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun ci karensu babu babbaka, inda suka rika bi gida-gida suna sace mutane a daidai lokacin da ake ruwan sama. Ba su kashe kowa ba, amma sun sace mutane akalla 50.
Kokki ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun ci karensu babu babbaka, inda suka rika bi gida-gida suna sace mutane a daidai lokacin da ake ruwan sama. Ba su kashe kowa ba, amma sun sace mutane akalla 50.
Kwamishinan Tsaro, Jin Dadi da Walwalar Jama’a, Emmanuel Umar, ya tabbatar da sace mutanen.
Sai dai kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN), ya jiwo Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Neja, Bala Kuryas, yana cewa jami’an tsaron hadin gwiwa sun yi nasarar ceto mutane tara daga cikin mutanen da aka sace.