@ katsina city news
Yan bindiga sun yi awon gaba da mai garin ummadau a Kan hanyar sa ta zuwa tarayyar tawagar kamfen din Dan takarar gwamna na jam iyyar APC.
Majiya mai tushe ta tabbatar ma jaridun katsina city news labarin.
Majiyarmu tace, Hanyar ummadau bata da kyau ko kadan.kuma wasu daga cikin masu fada aji na karamar hukumar a jam iyyar APC sun bada shawarar a kauce mata.
Majiyarmu tace shugaban karamar hukumar safana shine ya kafe sai an bi hanyar.
Ya kuma umurci duk wani maigari ya fito da jama arshi ya tarbi dan takarar.
Majiyarmu tace yanzu haka, ana can ofishin shugaban yan sanda na shiyyar Dutsinma ana tattauna yadda za a biyo ma lamarin.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245