misbahu Ahmad batsari
@ katsina city news
A cikin daren litanin kashe gari talata da misalin 2:45am wanda yayi daidai da 17-01-2023, wasu ƴan bindiga da ake zaton satar dabbobi ne da garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa suka kai hari unguwar katoge dake cikin garin Batsari ta jihar Katsina. Ƴan bindigai sun haura katanga sun dira gidan wani bawan Allah mai suna Mallam Abu-ƙasimu a unguwar ta katoge inda suka kutsa kai cikin ɗakin matarsa suka ce masa kai munafuki ka kulle gida ko? to bamu mabuɗi sai ya tashi zaune ya faɗi masu inda mabuɗin yake, wanda nan take ɗaya daga cikin su ya tsare shi, sauran biyu kuma suka je suka buɗe gidan sannan suka kore masa shanun huɗa guda biyu. Bayan sun fita da dabbobin tare da sauran waɗanda ke waje suna jiran ko ta kwana, sai wanda ya tsare shi yasa bindiga ya harbe shi, inda harsashi ya ratsa cikin shi ya fita ta gefe ya dagargaza mashi hannu, wanda yayi sanadiyyar rasa rayuwar shi.
Mutane da dama sun bayyana raayoyin su game da halin ko’in kula daga É“angaren gwamnati na rashin É—aukar matakin daÆ™ile irin waÉ—annan hare haren da suka zama ruwan dare a unguwannin dake arewacin Batsari, domin ko a makwanni biyu da suka gabata sun kawo irin wannan harin inda suka kashe wani Malam Tasi’u Mai ganda kuma suka tafi da dabbobin shi, haka ma sun shigo sunyi awon gaba da wata matar aure da garken dabbobi cikin satin da ya gabata duk a cikin garin na Batsari, amma dai babu wani mataki da aka É—auka na magance wannan matsalar, saima canza salo da suke na kawo hare haren.