Daga Misbahu Ahmad Batsari
@ katsina city news
A cikin tsakiyar watan maris na shekarar 2023 milladiyya ƴan bindiga suka yi garkuwa da wata mata mai suna Sahura Ɗahiru, wacce ke zaune a ƙauyen Ɗangaru dake cikin yankin ƙaramar hukum ar Batsari ta jihar Katsina.
Sun yi garkuwa da ita tare da ɗiyarta ƴar kimanin shekara ɗaya da haihuwa, inda ta kwashe sati ukku a hannun su ba tare da an biya kuɗin fansa ba, duk da cewa sun kira makusantanta domin neman a biya su kuɗi kafin su sake ta, amma dai haƙar su bata cimma ruwa ba domin sau ɗaya sukayi waya da su. kuma baa samu daidaito ba saboda su ba mawadata bane, kullu yaumun sai sun nemo na sawa bakin salati.
Daga ƙarshe ƴan bindiga sunyi yarjejeniya da ita cewa, tunda sun fahimci danginta basu son ta, to, amma duk da haka baza su kashe ta ba, saidai sun bata dama ta bar ɗiyarta ƴar shekara ɗaya wacce ke shan nono a hannun su, taje ta samo kuɗin fansa ta kawo masu sannan su bata ɗiyar, haka kuwa akayi.
yanzu haka matar tana nan ta dawo gida tana neman yadda zata haɗa kuɗin da suka yanka mata naira dubu ɗaari ukku (N300,000.00), sannan ta kai masu su bata ɗiyar ta yar shekara ɗaya.
Wasu makusantan ta sun bayyana mana cewa sunyi bakin ƙoƙarun su domin ganin sun fanso ta daga hannun ɓarayin dajin amma abun ya gagara saboda halin matsi da ƙangin rayuwa da suke fama da shi.
Katsina city news
@ Www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai
The links News
07043777779.