Muhammad Ali Hafizi @Katsina City News
A Safiyar Ranar Asabar ne 25/02/2023 yayi daidai da ranar da hukumar gudanar da zabe wato (INEC) ta ware ga ƴan nigeriya wajen ƙaɗa kuru’unsu ga ƴan takarkarun da suke so, An fara rarraba kayan zaɓen zuwa ga runhunan da za’a gabatar da zaɓen wanda ya haɗa da zaɓen shugaban ƙasa dana ƴan majalissu.
Mun samu damar ziyartar wasu wajejen da ake raba kayan zaɓen da misalin karfe taƙwas na safe inda muka tadda mutane daga kowane ɓangare suna amsar kayan zaɓen domin kaiwa a rumfunan da za’a gudanar da zaɓen.
A wani wajen kuma an samu tsaiko na raba kayan zaɓen saboda rashin isowar kayan zaɓen a wajen rabawar inda mutane sukai ta jiran zuwan su daga karshe kayan sun iso amma a cikin kurarren lokaci aka cigaba da rarraba zuwa ga kowace mazaɓa wannan ne ya sanya wasu daga cikin mazaɓun da zaa gabatar da zaɓen ba’a fara ba sai wajejen goma Wasu wajejen ma har wuce goman.
Mutane daga sassa daban-daban manyan su da yaransu maza da mata hadda ma miskinai sun fito inda suka cigaba da ƙaɗa ƙuri’unsu ga ƴan takarkarun da suke so na kowace jam’iya ba tare da wata matsala ba ko kuma wani zargi da dai sauransu.
An samu gudummuwar jami’an tsaro a kowace mazaɓa saboda gudun kada wata matsala ta tashi ko kuma wani yayi wani abu wanda ba daidai ba, jami’an tsaro sun bada gudunmuwa sosai ta kowace ɓangare wajen ganin an fara lafiya kuma an gama lafiya.
A kowace mazaɓa mutane tare da Ma’aikatan zaɓen sun bi duk wasu dokoki da INEC ta gindaya game da zaben, an samu fahimtar jun a ga kowane AGENT da yake wakiltar kowace jam’iya ba tare da hayaniya ba ko zargin junan su ba.
A zantawar da mukayi da wasu masu kaɗa ƙuri’a sun nuna mama yadda suka ji daɗi game da sabodon tsarin (VIVAS) ta hukumar zaɓe ta kawo wajen tantance masu ƙaɗa ƙuri’un cikin sauki.
Yawaicin sassan da aka gudanar da zaɓen an fara lafiya kuma aka kammala lafiya ba tare da faruwar wata matsala ba bisani kuma a wasu wajajen an samu yar matsala amma jami’an tsaro sun daidai ta komi.