
An biya jimillar kuɗi 352, 171, 190. 00, duk da haka babu irin waɗannan cibiyoyin a asibitocin jihar.
A ranar 2 ga Nuwamba, 2020, wannan dai kamfani na A.H.B Modandi Global Services an sake ba shi kwangilar siyan kayayyakin aikin asibiti domin cibiyoyin lura da mata da ƙanana yara guda 10. An fitar da jimillar 516, 554, 752. 00 a matsayin biyan kuɗin siyan kayayyakin.
Alhaji Mas’ud Abdulƙadir Ɗanguruf ya kasance cikakken mai goyon bayan jam’iyyar PDP wanda ya bayar da gudunmawa mai tsoka ga yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar a 2019. Shi ne ya kafa ƙungiyar goyon bayan Atiku a jihar Katsina ta Ɗanguruf. Ɗan kasuwan haifaffen jihar Katsina ya koma APC ne a shekarar 2022 ta hannun gwamnan Zamfara mai barin gado Bello Matawalle.
Rukunin kamfanonin Ɗanguruf na daga cikin manyan kamfanoni biyar da Gwamna Matawalle ke amfani da su wajen gudanar da ayyukan bogi, musamman gine-gine, saye da sayarwa na kayayyaki.
Kamfaninsa na Ɗanguruf Pharmaceutical Limited ya samu kwangilar gina masaukin Gwamna a ƙaramar hukumar Bukkuyum, a kan jimillar kudi naira 59, 141, 575. 00. An cire naira 35, 608, 185.13 daga baitul malin gwamnati aka kuma miƙa wa Mista Abdulƙadir domin wani aiki da har yanzu bai fara ba.
A ranar 22 ga watan Disamba 2022, an fitar da jimillar kuɗi naira 83, 878, 092. 62 daga asusun jihar Zamfara zuwa kamfanin Ɗanguruf Pharmaceutical Limited a matsayin kuɗin gyaran manyan asibitoci guda 10. Ba a bayyana sunaye da wuraren da manyan asibitocin suke ba.
Bugu da ƙari, a ranar 26 ga Disamba, 2022, Gwamna Matawalle mai barin gado ya saki jimillar kuɗi naira 1, 409, 435, 798.00 ga Ɗanguruf Pharmacy LTD a matsayin biyan kuɗin siyan kayan aikin asibiti ga asibitoci 10 da ba a bayyana ba. An bayar da kuɗaɗen ne ba tare da wani bayani kan sunaye da wuraren asibitocin da za a sayawa kayan aikin ba.
Wani babban ma’aikacin ma’aikatar lafiya ta jihar Zamfara da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa halin da ɓangaren lafiya ke ciki a jihar ya yi muni matuƙa da ban tsoro. Ya koka kan lalacewar ababen more rayuwa, rashin ƙwararrun ma’aikata, da rashin wadatar magunguna.

Ya kuma nuna matuƙar damuwarsa kan makomar fannin lafiya a jihar. “Halin da ake ciki yana da ban tsoro, yana nan a cikin kundi yadda aka kashe biliyoyin kuɗaɗe da sunan gyara, sabuntawa, sayan kayayyakin aiki, da kuma samar da magunguna. Amma komai sake taɓarɓarewa yake yi a kullum.
“Gwamnatin da za ta zo a Zamfara tana da babban aiki ja a gabanta; domin binciken kwangilolin da aka bayar da kuɗaɗen da aka fitar. Sama da kashi 90% na ayyukan da ake yi a fannin kiwon lafiya a Zamfara ayyuka ne na bogi waɗanda suke kawai a kan takarda ba a zahiri ba.
“Matawalle ya zaƙu wajen ganin ya cire sauran Naira miliyan dari biyar (500, 000, 000) cikin Biliyan Biyu (2, 000, 000, 000.00) da gwamnatin Tarayya ta biya na kayayyakin COVID-19. Ya riga da ya cire Naira 1, 500, 000, 000. Wannan wasu muhimman bayanai ne da ya kamata gwamnatin PDP mai jiran gado a jihar ta lura da kuma yin bincike sosai idan ta karɓi mulki a ranar 29 ga Mayu 2023.” Majiyar ta ƙara da cewa.

Duk da haifar da koma baya sosai da ya yi a jihar Zamfara, Gwamna Matawalle mai barin gado ya koma babban birnin tarayya ya tare yana kamun ƙafa wajen ganin gwamnatin tarayya ta naɗa shi a matsayin memba a gwamnatin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Saleh Zurmi shi ne Shugaban ƙungiyar Alternative Forum na Zamfara.