…amma ba gwamna Masari ya kawo wa hari da taɓarya ba, mun taimaka an damke shi, Cewar Jami’an Tsaro
A cikin satin da ya gabata ne, wani matashi mai suna Najeeb Umar Shehu dan shekara 24 a duniya ya kashe Kishiyar Mahaifiyarsa har lahira wadda tsohuwar Ma’aikaciyar Gwamnatin Jihar Katsina Ce Hajia Asiya Galadima tare da karya kafar Mahaifinsa, Inda ya yi amfani da taɓarya a Unguwar Goruba Road cikin birnin Katsina.
Majiyar Focus News Hausa Ta Nakalto Cewa Matashi Najeeb Umar, wanda ɗalibi ne a Jami’ar Gwamnatin Tarayya Dake Dutsinma A jihar Katsina kuma yana aji ukku ya sha furta cewa sai ya kashe Kishiyar Mahaifiyarsa domin yana ganin kamar tana yi masa ba dai-dai ba.
Matashi Najeeb ya zo gidan ranar Alhamis, ya shiga dakin Mahaifinsa da niyyar kulle shi domin ya samu damar aikata wannan mummunan aiki. Daga nan ya shiga kicin, inda ya dauko taɓarya ya shigo inda Marigayiya ke zaune tare da diyarta da wasu kuma ya garkame dakin. Daga na ya fara Cewa ” kin san na dauki alƙawarin wata rana sai na kashe ki, idan za ki iya tunawa, to yau zan kashe ki! Ba tare da bata lokaci ba, ya kwada mata taɓarya ga kai har sau biyu, nan take ta sume. Bayan da ta suma ya dawo dakinta ya tarar ba ta rasu ba, ya Kara buga mata taɓarya sai da ya tabbatar da ba ta Motsi.
Majiyar ta Tabbatar Mana cewa Najeeb Umar yana amfani da miyagun Kwayoyi,wanda ake ganin har da shaye-shaye da yake ya sa ya aikata wannan Aika-aikar
Da mahaifin da ya ji kara ta yi yawa ya fito, ya ganshi riƙe da taɓarya, a kokarinsa na kare yar uwar Matashin, ya buga masa taɓaryar a kafa shima nan take ya suma kuma kafarsa ta kare, Ita kuma ta ruga makwabta domin ceton ranta.
Yanzu haka Mahaifin Nasa, Alhaji Umar Shehu Balele, wanda Ma’aikaci ne a Ma’aikatar Ilimin Jihar Katsina yana kwance a Asibitin Koyarwa Ta Gwamnatin Tarayya Dake Katsina a bangaren Kula da Kashi. Ita kuma an yi Jana’izarta kamar yadda Addinin Musulunci Ya Tanada.
Bayan ya kashe Kishiyar Mahaifiyarsa ya karya kafar babansa ya fito kofar gida da taɓaryar yana cewa duk wanda ya matso kusa da shi sai ya kashe shi da Jama’a makwabta suka fito, sai ya ruga. Ba inda aka kama shi sai dai-dai wajen Jami’an Tsaro gidan Gwamnatin Jihar Katsina suka Taimaka aka cafke shi kuma suka damka shi ga Ofishin yan sanda na GRA dake cikin garin Katsina domin cigaba da bincike.
Allah Ya Jiƙanta Da Rahama Ya Baiwa Mahaifinsa Lafiya!