Daga Sulaiman Ciroma
A yunkurin cigaba da yakin neman zaben Dan takarar gwamnan jihar katsina Dr Dikko Umar Radda a karkashin jam’iyya mai ci ta APC ya samu shiga karamar hukumar Rimi da ke Jihar Katsina domin bayyana kyawawan manufofinsa ga al’ummar garin idan ya lashe zaben 2023 da ke karatowa.
Dubunnan mutane ne suka halarci gangamin taron daga ko wane lungu da sako da ke karkarar yayin da suka nuna goyon bayan su ga dan takarar a bayyane dari bisa dari.
Da ya ke jawabi dan takarar, Dr Umar Radda ga mutanen karkarar ya bayyana damuwarsa sosai ga irin yanayin da jama’a suka tsinci kansu musamman ta bangaren tsaro, sannan ya kara da cewa gwamnati na iya bakin kokarinta wajen ganin an kawo karshen ‘yan ta’adda. Dan takarar gwamnan ya cigaba da jaddada aniyarsa na dorawa daga inda gwamnati ta tsaya don tabbatar da jindadi da walwalar mutanen Jihar Katsina.