Daga Abubakar Tahir
Dayake lamarin Ambaliya ya kazanta a garin na Ganuwar Kuka inda cikin mintuna Sha biyar ruwa ya kusa gamawa da garin.
Haka tasa muka fara magana da abokanen aiki dake gidajen radio da jaridu kamar Bbchausa, Daily Trust,Humanangle, Liberty,JallaFm,Raypower dss domin dauko abinda yake faruwa kai tsaye.
Bayan isata garin Na gabatar da ID Card dina na aiki inda wasu matasa danakega sun waye suka biyo ni domin yin hirasa dasu.
Bayan na Dora musu Camera na nadi abun da suke da bukata sai na dan gusa kan domin cigaba da dauka.
Katsam sai naji an bugeni da karfi a kaina inda wayoyin dake hannuna Kira Infinix da Itel suka zuge cikin ruwa.
Dagowar da zanyi Ashe naga wanne dalili sai naji an ciga da dukana ta koina ana buga cikin wani rafi da suke Kira ruwan Makasa.
A haka sukayi ta dilmiya kaina suna dukana wasu suna cewa ku dake shi Nikwa inata kokarin nusar dasu ID card dina ina ce musu aiki nake.
A haka de wasu mutane sukayi maza suka hanasu Wanda daba Dan an kawomin daukin ba da tuni sun kasheni tunda a take wasu sun zare wuqaqe.
Haka aka kaini gidan Maigari ya bani Ruwa nayi wanka ya bani sabin Kaya na saka Inda ya bukaci na dawo na cigaba da aiki nace masa A’a.
Ya bada babura aka kawoni Hadejia inda a take na tafi babban asibitin Hadejia domin jinya.
Ya zuwa yanzu na dawo gida ina cigaba da karban magani.