• About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact
Friday, March 31, 2023
  • Login
Katsina City News
Advertisement
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
Katsina City News
No Result
View All Result
Home Sashen Hausa

Ya Zama Wajibi In Yi Magana A Nan

October 24, 2022
in Sashen Hausa
0
Ya Zama Wajibi In Yi Magana A Nan
0
SHARES
49
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Daga Al-Amin Isa

Ana samun dattaku a wurin yaro, ana samun dattaku a wurin babba. Kuma yawan shekaru ba su ne ke sa a ce wa mutum Dattijo ba. Akwai wasu halaye da ‘yan’adam ke dubawa a wurin mutum kafin ka ji sun ce: “Ai wane Dattijo ne,” ko da kuwa yana da karancin shekaru a duniya.

Na ga wani bidiyo da ke yawo a ‘social media’, wanda Ahmad Babba Kaita ke magana a taronsu na Jibia. Daga baya kuma na ga ya yi rubutu a shafinsa.

Ahmad Babba Kaita yana cikin wadanda muka yi gwagwarmayar murkushe PDP tun yana CPC, har aka yi maja muka dawo APC. Tsakaninmu akwai fahimta, akwai mutuntawa da girmama juna. A cikin APC kuma har yanzun muna da yawa wadanda muke da irin wannan alakar da shi, kamar mutane irin Maiwada Danmallam da Abdullahi I. Mahuta da Bishir Gambo, da sauransu.

Kuma Bahaushe na cewa, ko lahira wani yana cin albarkacin wani. Wannan ta sa nake ganin ko da Ahmad bai kalli shekaru da girman kujera da kuma alaka da suka yi a baya da Gwamna Aminu Bello Masari ba, to ko domin mu da ke tare da shi, zai yi raga masa.

A tarbiyyarmu ta Musulunci da kuma al’adar Hausa-Fulani, muna tashi daga gidajenmu da horon daga gun iyayenmu na mu girmama wanda yake gabanmu a shekaru, da kuma biyayya ga shugabanni.

Irin wannan tarbiyyar ta sa a al’ada ko a cikin gidajenmu muke cewa Babban Wa Uba. Akwai wasu kalamai da duk mutumin da Allah ya ba shi matsayi na shugabanci ba zai so jama’a su ji yana alakantuwa da su ba, balle a ce shi ne ke furta su.

Ya kamata ka gane kai Sanata ne a Nijeriya. Na san kuma ka san matsayinka a Order Of Protocol na kasar nan.

Ita kujerar da kake a kai, kuma kake yin takara kanta a 2023, sunanta Majalisar Dattawa. Ashe kuwa wanda har yake amsa sunan Dattijon Nijeriya, to ya kamata a ga halin dattaku tare da shi, ko da shekarunsa ba su kai na tsufa ba. Babu inda Dattijo ke furta irin wadannan kalaman da kake yi. Domin babu dattaku cikin irin wadannan kalaman.

Na ga cikin rubutun da ka yi kana kokarin ka rarrabe tsakanin Dattijo da Tsoho, domin ka yi ‘justifying’ kalamanka a kan Gwamna Masari.

To abin tambaya a nan shi ne, idan muka yi la’akari da matsayinka na Sanata (Dattijo a Nijeriya) kai a wane mataki za mu ajiye ka ke nan? Domin Dattijo ba ya zagi, ko furta kalaman da jama’a sun san ba su da alaka da Dattijo.

Ko da yaushe ana samun Dattijo da nuna halin girma, da kuma gabata. Ta haka ne wadanda ke biye da ko yaushe za su yi koyi da shi.

Na tabbatar da kai ma ba za ka ji dadin wani ya hau dirom ya yi maka irin wadannan kalaman ba, ko da tsaranka ne, balle wanda ka girma, ko kake gabansa a matsayi.

Shi dai Gwamna Aminu Belle Masari ba ya takara ko wacce iri a 2023, yanzu wa’adin mulkinsa bai wuce sauran watanni ba, ina ga yanzun abin da jama’a ke bukatar ka mayar da hankali a kai shi ne, bayani a kan ita sabuwar jam’iyyarka da kuma ‘qualities’ na dan takararku a PDP, wanda zai sanya masu zabe su ajiye namu na APC, su zabe ku.

Muna bukatar ka fito ka gaya muna a yanzu mene ne ya canza daga shi Yakubu Lado da ka ba mu labarinsa can baya? Wadanne ‘qualities’ ne suka yi ‘endearing’ naka ga Yakubu Lado yanzu?

Muna bukatar ka haska muna Dikko Umar Radda da Yakubu Lado da hujjoji kwarara da jama’a za su gamsu su ajiye maganarka a kan Yakubu Lado a 2019.

Na ga cikin rubutunka ka yi maganar abin da jama’a ya kamata su rinka yi wa tsoffin Gwamnoni irin Malam Umaru Musa, amma sai na yi mamaki da na ga ka tsallake Gwamna Ibrahim Shehu Shema, ka diro kan Gwamna Masari.

Shin shi Gwamna Shema ba ya cikin wadanda kake so a yi wa addu’a ne? Tun da shi Gwamna Masari ka ce babu addu’a tsakaninku to shi, Gwamna Shema fa? Ko shi ma har yanzun akwai jidalin kansa shi ya sa ka yi hikima ka zagaye shi domin ba ka son jama’a su gane abin da ke zuciyarka a kansa?

Kana da damar da za ka soki Gwamnatin Masari, mu kuma za mu iya kare ta, mu ba ka amsa, amma idan sukar mai tsafta ce.

Zan kuma so a ce ka koma yin ‘objective criticism’, domin mu kamar tallah ce za ka yi muna tun da dole za mu fito mu kare ta da hujjojin da za su gamsar da jama’a, amma Ahmad ba shi yiwuwa mu dawo a shekarunmu mu zama ‘yan jagaliya muna zagin juna a ‘social media.’

Ni a yanzun ina ganin ban yi wa kaina adalci ba idan na mai da maka da martani a irin yanayin da kai ka rufe ido ka ci mutuncin Gwamna Masari ba tare da ka yi la’akari da irin mutuncin da ke tsakaninmu da kai ba, mu da muka san ka, kuma muke tare da shi.

Share

Related

Source: Al'amin Isah
Via: Katsina City News
Previous Post

Kotu ta ƙwace wasu kadarorin Diezani Alison-Madueke a Abuja

Next Post

A watan Disamba ne za a kammala Aikin Titin sama da na karkashin kasa a Katsina -Yan Kwangila

Next Post
A watan Disamba ne za a kammala Aikin Titin sama da na karkashin kasa a Katsina -Yan Kwangila

A watan Disamba ne za a kammala Aikin Titin sama da na karkashin kasa a Katsina -Yan Kwangila

Recent Posts

  • On birthday, clerics pray for Tinubu, Nigeria in Abuja
  • Gwamna Masari ya Kaddamar da Kwamitin Miƙa Mulki ga sabuwar Gwamnati
  • Masari: Tinubu Na Bukatar Addu’a
  • Bashin Da Ake Bin Najeriya Ya Karu Zuwa N46.25tr —DMO
  • FEC Approves N59.78bn For Ogoni Cleanup Projects

Recent Comments

No comments to show.

Archives

  • March 2023
  • February 2023
  • January 2023
  • December 2022
  • November 2022
  • October 2022
  • September 2022
  • August 2022
  • July 2022

Categories

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • English
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina

Browse by Category

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • English
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina
  • About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact

No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In