Mahaifiyarmu ce ta bai wa ƙanwata guba tasha ta mutu, sannan ta umarceni, inyi zina da gawar kuma in sotse farjinta don inyi arziki- Inji wani matashi da ake zargin sa da kashe ƙanwarsa.
Wani matashi mai shekaru 29 mai suna Amos Olalere ya amince cewa shi da mahaifiyarsa suka haɗa baki suka kashe ƙanwarsa domin su yi tsafi na kuɗi.
Amos Olalere wanda gawurtaccen ɗan kutsen internet da aka fi saninsu da ‘yan “Yahoo” ya amsa laifinsa ne bayan da ya faɗa komar ‘yan sanda.
‘Yan sandan a jihar Legas suka damkeshi yayin wani sumame da suka kai unguwar Ikorodu dake birnin na IKKO.
Gaskiya Ta Fi Kwabo ta ruwaito cewa, lokacin da yake amsa tambayoyi a ofishin ‘yan sanda, Amos Olalere ya ce mahaifiyar sa ce ta umarce shi da ya zartar da kisan kai akan ƙanwarsa bayan da wani boka ya umurce su da hakan, idan har yana so ya riƙa samun nasara a sana’ar damfara ta Yahoo-Yahoo da ya ke yi.
“Mahaifiyata ce ta ɗauke ni ta kai ni wajen wani boka, inda shi kuma bokan ya shaida mini cewa matuƙar inason in riƙa nasara wajen sana’ar damfara ta Yahoo-Yahoo da nake yi, to ya zama wajibi in kashe ƙanwata da nake kauna sosai”
“Bayan wannan umarni da bokan nan ya bani nafi wata ɗaya inata juya wannan magana a raina, sai dai a wannan lokaci kullum mahaifiyarmu gayamini take yi , in aikata abin da bokan nan ya faɗa, in kashe ƙanwata, sannan inyi zina da gawarta kuma in sotse farjinta, kafin in ɗauki gawar in jefa a cikin kogi” inji Amos Olalere.
Matashin ya kuma bayyana cewa, mahaifiyarsa da kanta taje ta sayo maganin fiya-fiya na kashe ƙwari ta zubawa ‘yarta’ wato ƙanwata a cikin abinci, ta ci ta mutu sannan ni kuma na ɗauki gawarta na kwana ina zina da ita, bayan na gama na sotse farjinta, sannan na ɗauki gawar na jefa a cikin kogi.