Zainab Bagudu matar Gwamnan jihar Kebbi ta shiga cikin jerin sunayen masu neman muƙamin shugaban kungiyar masu kula da cutar Kansa ta Duniya UICC.
A wata sanarwa da shugaban kasa ya fitar, ya bayyana cewa Gwamnatin tarayya ta hanyar ma’aikatar Lafiya ta kasa da kuma ma’aikatar kula da harkokin kasashen waje zasuyi aiki tukuru domin ganin dakta Zainab ta lashe zaben da kungiyar zata gudanar.
Haka kuma shugaban ya taya murna ga matar Gwamnan na Kebbi bisa zamowa daya daga cikin ‘yan takarar shugabancin Kungiyar.
Source:
Radio Nigeria
Via:
Katsina