Farfesa Bichi ne ya bayyana haka a lokacin da yake ta’aliki ga Kasidar Darakta daga ma’aikatar Shirya zabe INEC, a taron Yaye Dalibai da aka koyama Sana’o’i da Cibiyar ta KVTC tayi a ranar Alhamis bayan gama Karanta Kasidar akan gudumawar Matasa Domin Samar da Zabe mai Inganci.
Shugaban jami’ar Gwamnatin Tarayya Dake Dutsinma Prof. Armaya’u Hamisu Bichi ya kara da cewa “Wanda Ya kafa wannan Cibiya Mutum ne, mai kokari kuma Mai kishin jama’a, kuma wadanda su ka assasa wannan cibiya Mutane ne masu kokari masu san taimaka ma Al’umma.
Prof. Bichi ya kara da cewa” a bangaren su na makaranta dake sunyi alkawali zasu Taimaka ma wannan cibiya da dukkanin abinda ta ke so, kuma wannan ba karamin al’amari bane, irin yadda wannan cibiya ta dukufa wajen taimakama matasa.