• About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact
Katsina City News
Advertisement
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
Katsina City News
No Result
View All Result
Home Sashen Hausa

Tsohuwa ‘Yar Shekaru 150 Ta Bayyana Yadda Sana’ar Tuwo-tuwo Ta Yi Mata Gata A Rayuwa.

Katsina City News by Katsina City News
December 15, 2022
in Sashen Hausa
0
Tsohuwa ‘Yar Shekaru 150 Ta Bayyana Yadda Sana’ar Tuwo-tuwo Ta Yi Mata Gata A Rayuwa.
0
SHARES
8
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Daga Mohammad A. Isa Da Ibrahim Tukur Garkuwa

Wata Dattijuwa ‘yar shekaru 150 a duniya mai suna Hajiya Asibi ‘Yardukusuru ‘yar asalin karamar hukumar Jibiya da ke jihar katsina, wadda yanzu take zaune a ‘yar kasuwa cikin birnin katsina, ta bayyana yadda sana’arta ta tuwo-tuwo wadda shafe shekaru aru-aru tana yi ta huce mata takaici a rayuwa har ma da doriya.

Hajiya ‘Yardukusuru ta bayyana haka ne a yayin da take amsa tamboyin wakilan tashar watsa labarai ta ‘Zamani Media Crew’ a cikin wani shiri mai suna “Hatsin Bara” na wannan Makon.

“Ban taba haihuwa ba, amma da sana’ar Tuwo na yi wa ‘ya’yan dangi guda Tara aure.

“Nan cikin garin katsina, na yi gida ya kai guda Biyar. Nan ‘yar kasuwa, na yi shaguna guda Hudu, amma yanzu ba ni da su duk na sayar. Kuma yanzu ina da gida, ga shi nan(kun gani) wanda nake ciki.” In ji ta.

Ta ci gaba da cewa, “Na mallaki motoci Shida; mota Urban guda Biyu, mota kwamfuta guda Hudu. Duk motar da ka gani a da an rubuta miyatti Allah, tawa ce.” Ta bayyanar

‘Yardukusuru ta ci gaba da cewar, ta je aikin hajji sau shida. A yayin da take bayyana da abin da ta fara kasuwancin nata da shi a matsayin jari tun a lokacin, ta ce duka-duka da naira dari biyu ne ta fara a matsayin jari a lokacin Sardaunan Sakkwato Ahmadu Bello.

“Na je Makka sau shida. Na fara da jari na jikka biyu (naira dari biyu) kudinmu na da. Ko zuwana Makka na farko abin da na biya jikka hudu da rabi, kudin guzuri jikka biyu da rabi. Haka na biya.”

Ta kara da cewar, daga baya ta kara da wasu sana’o’in masu alaka da sana’ar tuwo-tuwo din wanda take yi, kamar sana’ar sai da Shinkafa da Doya, da Naman Kaji da na Zabbi.

Hajiya Asibi ‘Yar dukusuru haifaffiyar garin sabon gari ce da ke a karamar hukumar jibiya, inda yanzu haka take zaune a unguwar ‘yar Kasuwa da ke cikin birnin Katsina.

Share

Related

Source: Katsina City News
Via: Katsina City News
Previous Post

“Majalisar Wakilai ta Tarayya ta amince da gina Jami’ar kimiyyar Lafiya a Katsina”

Next Post

Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna ya murkushe wata a mota

Next Post
Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna ya murkushe wata a mota

Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna ya murkushe wata a mota

Recent Posts

  • Tinubu To Rechannel Funds Into Education, Healthcare, Others
  • Dr. Dikko sworn in as Governor, takes over from Masari in Katsina State.
  • Tinubu Ya Nada Dele Alake A Matsayin Mai Magana Da Yawunsa
  • In inaugural address, Tinubu preaches unity, commitment to nation-building
  • Jawabin Farko a Matsayin Shugaban Æ™asa: Tinubu ya cire Tallafin Mai gaba É—aya

Recent Comments

No comments to show.

Archives

  • May 2023
  • April 2023
  • March 2023
  • February 2023
  • January 2023
  • December 2022
  • November 2022
  • October 2022
  • September 2022
  • August 2022
  • July 2022

Categories

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • English
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Interview
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Press Release
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Sashin Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina

Browse by Category

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • English
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Interview
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Press Release
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Sashin Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina
  • About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.

No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.