Tsohon shugaban rundunar sojin Najeriya a zamanin mulkin janar sani Abacha, Laftanar Janar Oladipo Oyeyinka Diya ya rasu.
Oladipo Diya wanda shi ne mutum na biyu mafi girman muƙami a zamanin mulkin sani Sani Abacha, a cikin watan Afrilu mai zuwa ne zai cika shekara 79 a duniya.
A wata sanarwa da É—ansa Barrister Oyesinmilola Diya, ya fitar a madadin sauran iyalansa, ya tabbatar da mutuwar tsohon babban jami’in sojin da safiyar ranar Lahadi.
An dai haifi Janar Oladipo Diya a garin Odogbolu na jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya, yana daga cikin dakarun da suka yi yaƙin basasar ƙaras, kafin ya zama babban hafsan sojin ƙasa na ƙasar, a shekarar 1993.
Ya kuma riƙe muƙamin mataimakin shugaban majalisar mulkin sojin ƙasar a shakerar 1994.