A ranar Litinin 2 ga watan Janairu Tsohon Sakataren Gwamnatin jihar Katsina kuma jigo a jam’iyyar PDP ya shiga Mazabar Wakilin Arewa A dake Cikin Birnin Katsina domin ƙaddamar da kungiyar Matasan PDP na yankin.
Taron da aka gudanar a Unguwar Madawaki ya samu halartar Wakilan ‘Yan takarar Majalisar Tarayya Hon. Aminu Chindo, da na jiha, tare da jiga-jigai na jam’iyyar PDP a Katsina da Mazabar ta wakilin Arewa A.
Da yake gabatar da Makasudin Kafa wannan Kungiyar, Shugaban Kungiyar Malam Bilya ya bayyana dalilin su na kafa kungiyar da kuma abinda ya kara masu karfin gwiwa na ganin kungiyar ta dore har zuwa zaben 2023.
Yace ” Anyi zaben shekara 2015 Allah bai bawa PDP Nasara ba, hakan yasa wasu daga cikin Abokai suka tuntubeni da cewa yakamata azo a samar da wata kungiya da zata tafi da Murya daya a cikin PDP don ganin hakan bata sake faruwa ba.”
Bilya ya bayyana mutanen da suka tuntubeshi kuma suka bashi jagorancin wanda ta kokarinsu da tuntubar wasu manya a jam’iyyar yasa gashi yanzu kungiyar tayi karfi da rassa a yankin na wakilan Arewa A. Injishi.
Da yake tsokaci a wajen taron tsohon Sakataren Gwamnatin jihar Katsina kuma Daraktan yakin neman Zaɓen Atiku da Lado Danmarke a jihar Katsina, dakta Mustapha Inuwa ya bayyana Kungiyar a matsayin mai ra’ayi da manufa wadda kwadai bai shamata kai ba. Yace “Alokacin da PDP ta faɗi zaɓe makwaɗaita da masu neman muƙami da basu iya adawa ba sukaita gudu don komawa sabuwar Gwamnati a dama dasu, amma ku a lokacin ma kuka yi nazari kuka ga yakamata ku sake Lale ku gyara abinda aka rasa domin daura damara dan neman sake dawo da jam’iyyar a kan mulki.” Yace lallai kam kun ciri tuta a irin wannan kokari.
Dakta Mustapha Inuwa ya gabatar da kungiyar gami da basu shedar karramawa a lokacin da itama kungiyar ta karramashi da lambar yabo.
Taron da ya gayyato masu ruwa da tsaki, a ciki kungiyar ta bayyana cewa zata samar wa Mazabar kuru’u masu tarin yawa bisa tsarin da sukayi.
Tun daga farko Jigo a jam’iyyar PDP Malam Ayuba Gambarawa ya bayyana jin dadi da gamsuwarsa ga kungiyar, gami da yabon kokarin da Dakta Mustapha Inuwa yake a cikin jam’iyyar PDP don ganin samun Nasarar zaben 2023, a karshe yayi fatan Alkhairi ga daukacin mahalarta taron gami da kira akan jajircewa da samar da ruwan kuru’u a lokacin zaɓe.