Nazarin jaridun Katsina City News, lokacin da aka zabi Alhaji Mannir Shehu Ruma, Shugaban Karamar Hukumar Kurfi dattawan garin sun dauka cewa a matsayinsa na Malamin makaranta zai yi kokarin ganin cewa doka da tsari sun tabbata a Karamar Hukumar, abubuwa na ta faruwa a Karamar Hukumar wadanda ke ba su mamaki, amma tsige mataimakin Shugaban Karamar Hukumar ba tare da bin dokar da take rubuce ba.
Ya kara tabbatar wa da mutanen garin cewa alwalarsa akwai lam’a. Mece ce ka’idar tsige mataimakin Shugaban Karamar Hukuma? Ga abin da doka ta ce;
- Ana iya tsige Shugaban Karamar Hukuma ko mataimakinsa a bisa tsarin wannan sashen.
- Rubutaccen korafi, wanda wasu mambobin na Majalisar Zartarwa suka sanya wa hannu.
- Zargin da ake yi wa wanda ake tuhuma za a sanar wa duk ’yan Majalisar a rubuce za a sake aika wa wanda ake zargi a rubuce don ya kare kansa cikin kwanaki bakwai.
- Bayan mako biyu da aika wa wanda ake tuhuma da takardarsa, Majalisar Zartarwa za su zauna su yanke shawarar ci gaba da tuhumar, ko kuma a kyale maganar.
- Idan har aka yanke shawarar a ci gaba da tuhumar, sai an samu amincewar kashi biyu cikin uku na ’yan Majalisar Zartarwar.
- In Majalisar Zartarwar ta amince da ci gaban binciken za ta aika wa Babban Mai Shari’a na Jihar domin ya kafa kwamitin mutane bakwai da za su binciki zargin.
- Wanda ake zargin zai iya kare kansa ko ya dauki Lauya da zai tsaya masa.
- Kwamitin yana da tsawon watanni uku ya kammala aikinsa da bayar da rahotansa.
- Idan kwamitin ya kasa tabbatar da zargin, daga nan aikin kwamitin ya tsaya.
- Idan wancan kwamitin da Babban Mai Shari’a ya kafa ya samu wanda ake zargi da laifin, Majalisar Zartarwar tana da tsawon makon biyu ta dau matsayar cire shi ko kyale shi. Idan har suka cire shi ya ciru har abada.
- In har aka bi wadannan ka’idojin babu wata kotu da za ta iya sauraren karar wanda aka cire.
Wadannan sune ka’idojin da ke cikin kundin dokokin kananan hukumomi na shekarar 2000 na Jihar Katsina, wanda Shugaban Karamar Hukumar Kurfi ya yi fatali da su wajen tsige mataimakinsa.
Katsina City News. www.katsinacitynews.com. Jaridar Taskar Labarai. www.jaridartaskarlabarai.com. The Links News. www.thelinksnews.com.