Bayanai sun ce zaɓaɓɓen shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai tattara ya koma masaukin Shugaban Kasa dake unguwar Maitama a Babban Birnin Tarayya Abuja, gidan da aka tanada wa duk zaɓaɓɓen Shugaban Kasa inda zai shafe sauran watannin da suka rage kafin a ratsar da shi.
Dalilin hakan shi ne domin samar mishi da wadatattun tsaro tare da fara karbar bayanan yadda harkokin gwamnati ke tafiya duk a cikin shirye-shiryen karban mulki.
Tuni dai aka fara gyaran gidan domin kammalawa cikin gaggawa.
Source:
Katsina City News
Via:
Katsina City News