A ci gaba da bibiyar sahihan rahotanni a hukumance da INEC ke saki, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Ahaji Bola Ahmed Tinubu na samun gagarumar rinjaye a jihar Ondo ya zuwa hada rahoton nan.
Ya zuwa yanzu INEC ta sanar da zaben kananan hukumomi 13 na jihar Ondo, inda Tinubu ya samu kuri’u 240,802.
A yayin da shi kuma Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 71,729, shi kuma Peter Obi na Labour Party ya samu kuri’u 24,097.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP kuwa, Injiniya Kwankwaso yana da kuri’u 433.
INEC na sanar da sakamakon ne a cibiyar tattara sakamakon zaben dake Akure a jihar.
Jihar Ondo na da kananan hukumomi 18, zuwa yanzu saura sakamakon zaben kananan hukumomi 5.
An tafi hutun rabin lokaci ya zuwa hada rahoton nan har sai 7 na yamma za a dawo.
©Rahoton Madogara TV/Radio