Taron ranar a Hausa, taro ne da aka kirkira a shekarar 2015 daga wasu zakakuran mutane karkashin jagoranci Mai kishin harshen Hausa da Hausawa Dan asalin jihar Katsina, Abdulbaki Aliyu, Wanda ya Saba gudana a ranar 26 ga watan 8 na kowace.
Taron na bana a gudana ne a dakin taro na munaj inda ya hada manya masana da daliban ilmi da masu kishi da kula da al’adun Hausa.

Bakin da suka halarci taron Ranar Hausa da ya gudana a Katsina
A bana taron ya dubi hanyoyin Al’adunmu za su iya taimakawa don samar da zaman lafiya. Taken Taron ya janyo halartar kakakin majalissar dokoki ta jihar Katsina, Alhaji Tasi’u Maigari zango da dan’majalissa Mai wakiltar karamar hukumar Katsina, Alhaji Ali Abu Albaba da Dan’majalissar Kankia Salisu Rimaye, da kuma Shugaban cibiyar Pleasent Library Engr. Dr Muttaka Rabe Darma.
Duba da irin gudunmuwar da wasu zakakuran mutane ke bayar wa wajen habbaka da bunkasa harshen Hausa, ya Sanya aka Karrama wasu fitattun mutane da suka hada da jajirtacce wajen binciken kwakkwafi, Kuma Shugaban rukunin jaridun katsina city news da Taskar Labarai da kuma Matasa Media Links, Malam Danjuma Katsina.