Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Fatima Sa’ad @Katsina City News
Da Yammacin ranar Alhamis ne, Jiga-jigai na Jam’iyyar NNPP mai kayan Marmari, suka shirya wata ganawa da bayyana goyon bayansu ga Dan takarar Gwamnan Katsina na Jam’iyyar APC Dakta Dikko Umar Radda a Ɗakin Taro na MUNAJ dake daura da gidajen Fatima Shema.
Taron wanda ya tattara ‘Ya’yan jam’iyyar NNPP daga Ƙananan Hukumomi 34 na jihar Katsina, gami da shugaban Jam’iyyar NNPP Hon. Sani Liti ‘Yan Kwani, Dan takarar Mataimakin Gwamnan jiha a NNPP Engr. Muttaƙa Rabe Darma, Dan takarar Sanata NNPP daga Shiyyar Daura, Sanata Abdu ‘Yandoma, da sauran magoya bayansu. Sai tawagar Dakta Dikko Umar Radda da suka halarci taron, a ciki akwai shi Dan takarar na Gwamna Dakta Dikko Umar Radda da Mataimakinsa Hon. Faruq Joɓe, Shugaban Yakin Neman Zaben na Dakta Dikko Radda, ARC. Ahmed Dangiwa, Umar tsauri, da Kwamishina Ruwa na jihar Katsina.
Shugaban yakin neman zaben na Dakta Dikko Umar Radda yayi cikakken bayani game da murna ta wannan hadin gwiwa tsakanin NNPP da APC, ya bayyana cewa sun ji dadi sunyi Farinci na ganin ‘Yayan Jam’iyyar NNPP sun fahimci Manufofin Dakta Dikko Umar Radda kuma har suka yadda su mara masa baya don cimma Nasara, yace sunyi Maraba da farinciki da komawarsu APC.
Saidai a tsakar taron, magoya bayan Jam’iyya NNPP sun bayyana cewa an yaudaresu saboda ba a sanar dasu abinda za’ayi ba, kuma anyimasu balilliba. Inda suka tada hatsaniya, wanda daƙar aka shawo kansu.
Da Dan takarar Mataimakin Gwamna a karkashin Jam’iyyar NNPP Engr. Muttaƙa Rabe ya amshi abin magana ya bayyanawa magoya bayansu cewa, su basun zo nan don su koma NNPP ba, a’a sam sunzo ne don su bayyana cewa zasu marawa Dikko Radda baya, a APC don ya zama Gwamna ba don komai ba sai dan ya cancanta kuma mutum ne, mai sanin Yakamata da Ilimi. Yace suna nan jam’iyyarsu ta NNPP kuma zasu ci gaba da tarairayarta har takai lokacin da zasu moreta.
Dakta Dikko Umar Radda ya gabatar da Jawabin godiya da nuna jin dadi bisa wannan yarda da Amincewa da magoya bayan NNPP sukai masa, kuma ya tabbatar da Insha Allah ba zai basu kunya ba.
Saidai bayan taron ya tashi, magoya bayan na NNPP sunyi ka-ce-na-ce harda bige-bige, kafin wani dan lokaci sai ga Dan takarar Gwamna a NNPP Engr. Nura Khalil ya bayyana a wajen inda ya ƙaryata zancen kuma yace shi ba da yawunsa ba. Wannan magana tasa bata yiwa magoya bayan Muttaƙa Rabe Dadi ba, inda anan aka fara bawa Hamata Iska, hatta ‘yan takarar suma suka sanya hannu.
Abin ya tsagaita duk da babu wasu jami’an tsaro a wajen, mun samu zantawa da Dan takarar Gwamna Engr. Nura Khalil, ya sheda wa Katsina City News cewa, ba da yawunsa ba bai sanda maganar ba, ankirashi ne, akace Engr. muttaƙa da Shugaban Jam’iyyar NNPP zasu cefanar da Takararsa. Shine yazo wajen don ya ƙaryata zancen. Nura Khalil ya bayyana cewa har yanzu yana kan takara kuma zasu dauki mataki akan masu yunkurin Lalatamsu jam’iyya a cikin satinan Sana ya bayyana jin dadinsa na dage zaben da akayi na Gwamna, yace hakan zai basu damar gane Munafukai jam’iyyar NNPP a Katsina.