A ranar Litinin 16/01/2023, mutanen su ka fice daga Jam’iyyar ta PDP, ya yin da Dan takarar Gwamnan Jihar karkashin tutar Jam’iyyar Dr. Dikko Umar Radda ya ziyarci karamar hukumar Funtua gangamin yaÆ™in neman zabe.
Da yake gabatar da jawabinsa Dr Dikko Radda ya bayyana manufofin shi, inda yasha alwashin kawo karshen matsalar tsaro data addabi wasu sassa a Jihar katsina, tare da inganta harkokin noma, Lafiya da ilimi da samar da ayyukan yi ga matasa musanman wajen basu horo don a dama dasu wajen samar da tsaro.
Daga karshe yaja hankalin Al’ummar karamar hukumar Funtua da suyi hankali da Æ´an damfarar siyasa wanda zasu zo masu karya da matsalar tsaro, saboda haka idan sun zo su tambaya akwai kudin tsaro na shekara bakwai da rabi da aka bada ina aka Kai su, ya kuma yi kira da a fito ranar zabe a zabi jam’iyyar Apc tun daga sama har kasa.
Mutane da dama ne suka tofa albarkacin bakinsu daga cikin akwai Dan takarar sanata na shiyyar Funtua Hon muntari Dan Dutse, tsohon Sanata na shiyyar ta Funtua sanata Abu Ibrahim.
Sauran sun hada da shugaban karamar hukumar Funtua, tshohon Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar Apc Alh. Ibrahim Masari, mataimakin shugaban jam’iyyar Apc Jihar katsina Alh. Bala Abu Musawa.
Shugaban jam’iyyar Apc na Jihar katsina Hon Sani JB Daura, Wanda shi ne ya amshi wadanda su ka sauya shekar a karkashin jagorancin Hon. Hassan Damana.
Kaddamar da gangamin yaÆ™in neman zaben wanda ya gudana a filin wasa na makarantar firamare ta Aya, ya samu halartar din bin magoya bayan jam’iyyar Apc Maza da Mata da sauransu.