Daga Muhammad Aminu Kabir
Adai dai lokacin da Mutane da dama suke ruguguwar barin garuruwan da suke domin zuwa jihohin su suyi zaɓe adai dai lokacin kuma suke cin karo da aƙuba a tashoshin mota sanadiyyar rashin tsabar takardun kuɗi.
Rashin Sababbin takardun kuɗi ya tsunduma Mutane da dama cikin rashin tabbas yayin da kuma masu tsofaffin takardun kuɗi ma aka ƙi karɓar nasu duk kuwa da yake cewa fadar Shugaban ƙasa da babban bankin ƙasa sun Amince cewa a ci gaba da karɓar tsofaffin takardun kuɗin amma dai har yanzu Mutane suna ɗari ɗarin karɓar su.
Matafiya da dama sukaje tashoshin mota mallakin Gwamnatin Jihar Katsina a garuruwan da suke da zummar tahowa gida sun haɗu da wannan ƙalubale, Inda ga motoci amma an bayyana cewa wai Operation Manager daga KATSINA yace ba’a amsar transfer ba’a kuma amsar tsofaffin takardun kuɗi.
Abin mamaki kuma gwamnatin jihar Katsina na ɗaya daga cikin Gwamnatocin da suka kai gwamnatin tarayya ƙara a kotu domin a cigaba da amsar tsaffin kuɗi amma ga motochin hukumar Gwamnatin Jihar basa karɓar tsofaffin takardun kuɗin idan kabasu, Duk dako kotu ta bada Umarnin amsa, gwamnatin tarayya ta bada umarni amsa, Central bank ya bada umarni karɓa, Amma abun mamaki KTSTA idan ka basu basa karɓa komi nene dalilin hakan Allah masani.
Kodai a jiya Motocin Hukumar daga jihar Kaduna zuwa Katsina sun ki amsar tsofaffin takardun kuɗin kazalika transfer, dalilin da yasa Matafiya da dama halin ƙunci, munyi ƙoƙarin jin ta bakin Babban Manajan hukumar ko akwai dalilin da yasa basa karɓar tsofaffin takardun kuɗin sai dai ya aiko da saƙon cewa yana Meeting har kawo wannan lokacin kuma bai maido kira ba.
Sai dai a wuri ɗaya kuma Sakataren hukumar Sufurin ta jihar Katsina Alh. Ibrahim Ahmed Keegan ya bayyana cewa a babban Offishin Hukumar dake nan Katsina suna amfani da P.O.S domin sauƙaƙa ma Matafiya amma dai a wajen jihar ne basu da pos ɗin batun rashin karɓar transfer kuma yace gaskiya ana samun damuwa da ita ne mafi yawan lokaci ta kan ɗauki lokaci bata sauka ba a wani lokacin ma Ƴan 419 suna amfani da yanayin suce sun tura alhalin basu tura ba, sai dai yace baida Masaniya akan mi yasa ba’a amsar tsofaffin takardun kuɗin amma dai zai bincika.
Haƙiƙa an wahalar da jama’a a motochin gwamnati kuma Mutanen katsina wanda da dama suna tafiya ne KATSINA domin suyi zaɓe, Amma idan kazo da tsaffin kuɗi sai suƙi karɓa.
Kiran da muke ga wannan Hukumar dama Gwamnatin Jihar Katsina shine su dubi Lamarin nan domin samar ma Mutane mahita adai dai wannan yanayin da aka rutso na matsin tattalin arziki sanadiyyar wannan rashin takardun kuɗin a hannun jama’a.