
Rundunar Sojin ruwa ta Najeriya ta ce ta ƙona wani kwale-kwale da ta kama ɗauke da gangar man fetur 273 na sata a cikin ruwan Calabar da ke kudu maso kudancin ƙasar.
Yayin da yake jawabi ga manema labarai a birnin Calabar, babban jami’in sansanin sojin ruwan da ke birnin Laftanar Isaac Ayogu ya ce an kama mutum shida waɗanda ake zargi da satar man a kan hanyarsu ta zuwa tashar ruwa ta Agbani.
Ya ƙara da cewa wannan farmaki na daga cikin tsare-tsaren da rundunar sojin ruwan ƙasar ke gudanarwa ƙarƙashin umarnin babban hafsan hafsoshin tsaron ƙasar Janar Lucky Irabor, na cewa a lalata duk wani kaya da aka kama da ke da alaƙa da sata.
Laftanar Ayogu ya tabbatar da cewa rundunar sojin ruwan ƙasar ta sha alwashin kawo ƙarshen ayyukan masu satar mai.
Ya ƙara da cewa tuni suka miƙa mutane shida da suke zargi da satar man hannun hukumar tsaro ta Civil Defence domin gurfanar da su a gaban kotu.