Makonni biyu kafin zaɓen 2023, Hukumar Tsaron Sojojin Najeriya ta ƙaryata raɗe-raɗin cewa wasu sojoji na tsara yadda za su kifar da gwamnatin farar hula.
A ranar Asabar Hedikwatar Tsaro ta ce a yi watsi da rahotannin ƙarya na masu cewa sojoji na shirin yin juyin mulki. Sun ce wanda ƙirƙiro wannan maganar ‘mummunar farfaganda ce kawai’ ta wasu ‘marasa son zaman lafiya.’
Daraktan Yaɗa Labarai na riƙo na Hedikwatar Tsaro, Burgediya Janar Tukur Gusau ne ya sanya wa sanarwar hannu a Abuja.
Ya ƙara da cewa Rundunar Sojojin Najeriya ta damu sosai ganin yadda wasu ɓatagarin ‘yan siyasa ke zubar da ƙimar su su na shiga harkokin masu son tarwatsa Najeriya.
“Ɓatagarin da su ka riƙa watsa wannan ji-ta-ji-tar cewa wai wasu sojoji na shirin juyin mulki, sun gana da wani ɗan takarar shugaban ƙasa, domin a kawo ruɗun dagula zaɓe da cunno wa ƙasar nan wutar rikici.
Gusau ya ce masu son kawo tashin hankali a ƙasa kaɗai za su iya watsa waɗannan ƙarairayi don cimma wani buri na su na siyasa.
Daga nan ya ce za a kama su domin su fuskanci doka da hukuncin da ya dace da su.
“Ya kamata jama’a su sani Sojojin Najeriya ƙwararru ne kuma mabiya dokokin da ke cikin kundin tsarin mulkin Najeriya. Kuma ba za su taɓa yarda su shiga cikin duk wai mugun shirin ƙulla wa ƙasar nan sharrin da zai dagula dimokraɗiyya ba.
“Kuma sojojin Najeriya ba su goyon bayan duk wani ɗan takara. Kuma Sojojin Najeriya za su tabbatar jami’an tsaron da su ka dace sun gayyaci waɗanda su ka watsa wannan ƙarairayi an gayyace su domin su bayar da ba’asi.”
A ƙarshe Gusau ya yi kira da shawara ga jama’a su yi watsi da wannan ji-ta-ji-tar, kowa ya ci gaba da harkokin da ke gaban sa.